✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta’aziyya: Tsakanin Garba Gashua da Sule Bello a zamanmu a HCB

La’akari da fikira da kuma fasahar da Allah Ya ba shi na waken baka ta sa Farfesa Sule Bello ya sa aka yi mi shi…

Farkon haduwarmu da shi a karshen shekarun 1980 ne a gidan talbijin na CTV67 (ARTV a yanzu) a sabon ginin dakin dauka da kuma gabatar da shirye-shirye na zamani da gwamnan jihar na farar hula a waccan lokaci Muhammadu Abubakar Rimi ya gina a unguwar Hotoro.

A lokacin wannan ginin da kuma dan uwansa na watsa shirye-shirye sune gine-gine biyu kadai a wannan katafaren fili sai kuma doguwar eriyar tashar talbijin din da a lokacin ta kere duk wani gini mai tsawo a birnin Kano.

Duk da cewa na dade ina mu’amilla da tashar tun tana cikin gidan gwamnatin jihar Kano, a inda muke fita wasan kwaikwayon zaman duniya, a wannan karon na zo gidan ne a matsayin dalibi mai neman sanin makamar aiki daga makarantar koyon dabarun aikin talbijin ta Jos.

Shi kuma Garba Gashuwa yana daya daga cikin kananan ma’aikata a wajen.

La’akari da fikira da kuma fasahar da Allah Ya ba shi na waken baka ta sa Farfesa Sule Bello ya sa aka yi mi shi sauyin aiki daga tashar talabijin din zuwa Hukumar kula da Tarihi Da Al’adun Gargajiya ta jihar Kano (HCB) a 1987 a inda Farfesan yake shugabanta.

Ya kuma sa aka ba shi ofis a karkashin sashen kula da harshe da kuma adabi (Language and Literature) aka kuma samar masa duk abin da yake bukata don fitar da basirarsa.

Ni kuma a lokacin an dauke ni a sashen kula da ala’adu da kuma gabatar da wasannin kwaikwaiyo da sauran wasanni na gargajiya.

Garba Gashuwa na daya daga cikin hazikan mawakan da suka taimakawa jam’iyyar PRP kafa mulki a jihar Kano da Kaduna a shekarar 1979 bayan ta kayar da jam’iyyar NPN wacce ta lashe sauran jihohi da kuma kafa gwamnatin a matakin tarayya.

Hakan ta sa duk da cewa ba dan asalin jihar Kano bane, aka ba shi abin aiki a tashar talabijin da gwamnatin jihar ta kafa, sai dai sakamakon rashin karatun zamani da shaidar karatun boko ta sa ya aka ajiye shi a matsayin a karamin ma’aikaci masinja da kuma mai yin share-share.

Laka’ari da wannan nakasu da kalubalen rayuwar aikin gwamanti da kuma son daga likafarasa don tafiya da zamani, Farfesa Sule Bello shugaban hukumar ya sa sunansa a wani kwas na sanin makamar aiki a Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya.

Karatun kwas din na tsawon watanni shida zuwa shekara ne a Cibiyar Nazarin Al’adun Gargajiyar Al’ummar Najeriya (CNCS), kuma ma’aikatan hukumomin kula da tarihi da al’adun gargajiya na jihohin kasar nan ne kadai ke yin sa.

Karatun na iya kai wa ga matakin digiri in har mutum yana so ya ci gaba. Domin ta wannan hanyar ce, aka ce jarumai irin su marigayi Kasimu Yero da Danjuma Katsina, Kasagi suka kai ga samun matakin digiri na daya da biyu a jami’ar.

Farfesa Sule Bello ya kira ni ya kuma fada min cewa, ni ma ya sa sunana da kuma abokin aikina Bala Sabo don yin wannan kwas din.

Ya kuma yi hakan ne a cewarsa, ba don mu kara sanin makamar aiki ba, sai don mu taimakawa Garba Gashuwa ya yi karatun don ya samu takardar shaidar da za ta taimakawa baiwar da Allah Ya ba shi a hukumance saboda gaba.

Sai dai kafin lokacin tafiya karatun aka daga likkafar Farfesan zuwa Hukumar Kula da Al’adun Gargajiya ta Kasa (NCAC).

Da tafiyarsa wanda ya gaje ya cire sunayenmu ni da Garba ya sa wasu.

Daga baya an sauya min wurin aiki zuwa sashen bincike da adana tarihi a bangaren adana bayanai na hoto na kuma bidiyo.

Aka kuma dauke na daga ofishin hukumar na gidan be minista na kan titin Sakkawato (Sokoto Road) zuwa hedkwata, wanda a lokacin yake kusa da gidan gwamna, a nan muka zama makwabtan juna ofis da ofis.

Cikin tsarin aikinmu na adana tarihi mun yi hira da marigayin kan tarihin rayuwarsa a inda muka dauki tsawon wasu kwanaki muna yi.

Mun kuma cika kaset-kaset na bidiyo mai tsawon minti 90 na VHS sama da guda biyar da hirar.

Inda ya bayyana mana yadda ya soma waka da irin gwagwarmayar da ya sha na kasancewarsa tsohon dan NEPU da kuma sanadiyyarsa zuwa Kano da sauran al’amuran da suka shafi rayuwarsa har zuwa waccan zamani.

Hakika Garba Gashuwa fasihi ne wanda rashin karatun boko bai zama nakasu a gare shi ba, kasancewarsa tsohon gardi duk rubutunsa na wakoki da ajami yake yin su kuma cikin zayyana da ado mai kyau kamar rubutun Kur’ani na hannu.

Ya kuma rubuta da rera wakoki da yawa kan muhimmancin kula da tarihi da kuma al’adu a inda yake gabatarwa a tarukan hukumar tare da ‘yan amshinsa suna yi da tafi.

A wata ziyarar aiki na shugaban kasa Ibrahim Babangida zuwa Kano aka sa ya yi masa waka da kida, wanda kuma shi ne na farko a tarihin wake-wakensa a wani sabon salo na hukumar domin murnar zuwan shugaban na kwanaki bakwai jihar a hukumance.

Garba Gashuwa ya kuma rera masa wakoki masu dadi wanda aka yi ta sawa a gidajen rediyo wanda ya dada fito da shi ga idon duniya da kuma basirarsa.

Ya kuma yi irin wadannan wakoki na fadakarwa a lokacin da gwamnatin mulkin sojan ta kirkiro da jam’iyyun siyasar SDP da kuma NRC.

Barinsa aikin gwammati ya koma yin wakokin siyasa ka’in da na’in a inda ya wake wasu fitattun ‘yan siyasa da ke takara a kamar Magaji Abdullahi (“Kai za ka yi gwammna baba Magaji Abdullahi SDP ce ta tsai da kai da ka da gaba) da ke takarar gwamna da kuma sauransu.

Ganina na karshe da shi, shi ne a wani lokaci da na je unguwarsu ziyara na kuma ratsa muka gaisa, ya kuma gabatar da ni ga dansa Musa wanda ya gaje shi a waka amma na zamani a salon ‘yan sahwa na Sudan, ya kuma bude abin ofishi a garajen gidansa a unguwar Sheka makaranta.

Allah Ya jikansa, Ya sa ya huta. Ya kuma inganta abin da ya bari. Amin