Manyan mutane da hukumomi da kungiyoyi a sassan Najeriya na ta aika sakon ta’aziya ga iyalan daya daga ministocin kasar a jamhuriya ta farko Alhaji AbdulGaniyu Folorunsho Abdul-Razaq SAN (OFR).
Mamacin shi ne mahaifin Gwamnan Jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazak kuma ya rasu a daren Juma’a yana da shekaru 93 a Abuja bayan rashin lafiya.
Sanarwar da daya daga cikin iyalan mamacin Alimi Abdulrazak ya sanya wa hannu ta ce, “Cikin kankan da kai da mika wuya da lamarin Ubangiji, iyalan Abdulrazak na masarautar Ilorin ta jihar Kwara suke sanar da rasuwar daya daga cikinsu, Alhaji AbdulGaniyu Folorunsho Abdul-Razaq SAN (OFR) mai shekaru 93 a Abuja.
“Matawallen Ilorin kuma Tafidan Zazzau ya rasu da misalin biyu na daren ranar Asabar, 25 ga watan Yuli, 2020.
“Lauya na farko a Arewacin Najeriya, marigayin ya rasu ya bar matarsa, Alhaja Raliat AbdulRazaq ‘yar kimanin shekaru 90, ‘ya’ya, ciki har da gwaman jihar Kwara mai ci, Abdulrahman Abdulrazak.
Kakakin Majalisar Dokokin jihar Kwara, Yakubu Danladi-Salihu da jam’iyyar APC reshen jihar na daga cikin wadanda suka fara aika sakon ta’aziya.
Shi ma shugaban APC reshen jihar, Bashir Omolaja Borinwa da shugaban kungiyar cigaban Masarautar Ilorin, Aliyu Uthman, duk sun bayyana alhini tare da cewa rasuwar babbar rashi ce.