Amurka ta ce ta tabbatar ta’asar da sojojin Myanmar suka yi wa ’yan kabilar Rohingya marasa rinjaye kisan kare dangi ne kuma laifukan cin zarafin al’umma.
Dubban daruruwan ’yan Rohingya yawancinsu musulmi sun tsere daga Myyanmar tun shekarar 2017 bayan da sojoji suka yi musu dirar mikiya.
A yanzu aka shigar da karar kisan kare dangi a gaban Kotun Duniya da ke Hague a Holland.
Gidan Rediyon Jamus ya ce a ranar Litinin ake sa ran Sakataren Harkokin Wajen Amurka Anthony Blinken zai sanar da shawarar ayyana dirar mikiyar a matsayin kisan kare dangi.
’Yan Rohingya kimanin 850,000 suke zaune a sansanoni a makwabciya kasar Bangladesh wasu 600,000 kuma suka ci gaba da zama a Rakhine inda suka baiyana azabtarwa da cin zarafi da ake yi musu.