Gwamnatin Jihar Borno, ta wanke tare da yi wa wasu mutum 500 da ake zargi da hannu a ayyukan ta’addanci afuwa a jihar.
Kwamishiniyar Harkokin Mata ta jihar, Zuwaira Gambo ce, ta bayyana haka a yayin da ta ke mayar da martani ga wasu mata da suka yi korafi game da ci gaba da tsare mazajensu da ‘yayansu.
Ta ce an saki mutane rukuni-rukuni ne, kuma har an mika su ga gwamnatin Jihar Borno.
Kazalika, ta ce a baya-bayan nan gwamnatin jihar tn saki mutum 28 daga cikin wadanda aka samu ba su da hannu a ayyukan ta’addanci.
Jihar Borno da ke Arewa Maso Gabas, ta shafe sama da shekara 13 tana fama da ayyukan ta’addanci na kungiyar Boko Haram mai ikirarin jihadi.
Hare-haren ta’addancin ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da sanya wasu da dama zama ‘yan gudun hijira.