✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jami’an tsaron Ghana sun binciki dan Majalisar Najeriya kan zargin ta’addanci

Jami'an tsaro sun yi wa dan majalisar Najeriya binciken kwakwaf a kasarsu.

Hukumomin tsaro a kasar Ghana na bibiyar ’yan Majalisar Tarayyar Najeriya saboda zargin da ake wa dayansu da daukar nauyin ’yan ta’adda masu neman ballewa daga Najeriya.

Dan Majalisar Wakilai, Ben Roland Igbakpa, ne ya bayyana haka, yana mai cewa jami’an tsaron Ghana sun yi masa binciken kwakwaf a lokacin da ya ziyarci kasarsu, washegarin jawabin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya zargi wani dan majalisar da bai bayyana sunansa ba da daukar nauyin ta’addanci.

“Ranar Asabar na je halartar wani daurin aure da aka gayyace ni a kasar Ghana. Mai girma Shugaban Majalisa, abin da jami’an tsaron Ghana suka yi min zai ba ka mamaki — Tsare ni suka yi na tsawon awa hudu cewa akwai abin da suke so su tabbatar.

“A karshe dai ban samu daurin auren da ya kai ni kasar ba; Sai bayan da na shafe awa hudu da ina zaman jira, wani jami’in tsaro ya zo ya ce da ni in yi hakuri, sun samu sanarwa ne daga Najeriya cewa akwai wani dan majalisa da ke daukar nauyin ’yan ta’adda shi ya sa suke aiki saboda kar wani dan majalisar ya je kasarsu ya tayar da fitina. Haka nan na dawo da sanyin gwiwa,” inji shi.

Don haka dan majalisar ya bukaci Shugaba Buhari ya fallasa sunan dan Majalisar da ke da hannu a ayyukan ’yan a-ware, ba kamar yadda ya yi musu kudin goro ba, lamarin da ya sa hukumomin tsaron Ghana sanya ’yan Majalisar Tarayyar Najeriya a cikin jerin mutanen da ake bibiyar lamairnsu.

“A matsayinsa na uba, kamata ya yi ya fadi suna ya kuma kunyata duk dan da ke neman kawo rabuwar kai, amma Shugaban Kasa bai fadi sunan mutumin ko mutanen ba, sai ya yi mana kudin goro mu 469.”

Bayan sauraron jawabin nasa, Shugaban Majalisar, Femi Gbajabiamila , ya ce majalisar ta ji koken nasa kuma za ta sake waiwayar sa.

Idan za a iya tunawa a jawabin bikin zagayowar ranar samun ’yancin Najeriya ne Buhari ya yi zargin cewa akwai wani dan Majalisar Tarayya da ake bincika a kan zargin sa da daukar nauyin ayyukan ’yan a-ware.