✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta’addanci bai da madogara a Musulunci (2)

Masallacin Juma’a, na Nagazi, Okene, Jihar Kogi A yau masu wuce iyaka sun zamo marasa hakuri da tarihi kuma sun zamo marasa hakuri da sa…

Masallacin Juma’a, na Nagazi, Okene, Jihar Kogi

A yau masu wuce iyaka sun zamo marasa hakuri da tarihi kuma sun zamo marasa hakuri da sa ran samun rahamar Allah. Sheikh Abdulhakim Murad ya yi bayani kan wannan batu a cikin wani rubutu nasa mai suna “Biyayyar Musulmi da yadda suke.” Na tsakuro wasu muhimman bayanai da ya rubuta kamar haka:
“Samun nasara a Makka ba ya zo ne ta hanyar fusata da gaggawa da firgitawa da barna a lokacin wahala ba, a wasu lokuta Musulmi sun shiga tsaka mai wuya, sun kasance karamin tsibiri a tsakiyar tekun kafirci da arnanci. Sun samu nasara ce ta hanyar kwantar da hankalinsu da biyayyarsu. Ibnu Juzi ya bayyana mana cewa wannan yana nufin karfin halinsu da sadaukar da kai da kuma tausayawarsu. Wadannan baiwoyi ne na dogaro ga alkawarin Allah a lokacin da ake cikin tsanani. Sabaninsu su ne wadanda aka bayyana da: “Suna mugun zato ga Allah,” wadanda malama tafsiri suka ce, hakan na nufin zargin Allah Zai kunyata muminai. Alhali Allah Madaukaki ba Zai kunyata muminai ba, kamar yadda Ya sha nanatawa a cikin Alkur’ani Mai girma: “Kuma kada ku yi rauni, kuma kada ku yi bakin ciki, alhali kuwa ku ne mafiya daukaka, idan kun kasance masu imani.” (k:3:139).
An saukar da wannan aya ce  bayan nasarar da kafirai suka samu kan Musulmi a yakin Uhudu. Don haka matashi mai gaggawa, da kan yi amfani da rabin hankalinsa wajen fassara Sunnah da muguwar fassara tunaninsa game da tarihin al’ummarsa shi ne an yi watsi da ita – wato Allah Ya yi watsi da ita kacokan.” Wannan shi ne takaitaccen abin da na cirato daga rubutun Sheikh Abdul Hakim Murad.
Ya ’yan uwa Musulmi! Duk wanda ya yi ta’addanci a kan mutane mai laifi ne koda da wane suna suka kira kansu. Fushi da kiyayyarsu ne suke rinjayarsu. Tunaninsu ya sa sun makanta daga yakini da dogaro ga Allah, don haka suke yanke wa kansu hukunci. Kuma babu wata nasara da za su samu ta haka. Wajibi ne mu karantar da matasanmu hadarin batattun kungiyoyi da darikoki.
 
Huduba ta Biyu:
“Subhanallah walhamdu lillah wa la haula wa la kuwwata illah billah.”
’Yan uwa maza da mata! Me za mu yi rigakafi ko hana sake tashin bama-bamai, kuma ta yaya za mu dakatar da bata kyakkyawan sunan Musulunci?
1.    Na farko, idan muka san akwai wanda yake kokarin kai hari, ko yana da hannu a ayyukan ta’addanci, mu hanzarta sanar da hukumomin tsaro. Aiki ne da Musulunci ya wajabta mana, kuma nauyi ne a kanmu a masayinmu na ’yan wannan kasa tamu Najeriya, kuma hakan zai taimaka wajen kare rayuka da dukiyar kowa da kowa. Najeriya kasarmu ce, bai kamata mu lamunci aikin ta’addanci ba ko daga wane bangare ya fito, kuma bai kamata mu kawar da kai ko mu toshe kunne ba. Mu ko wani makusancinmu yana iya zama wanda harin zai shafa ko wanda suke son kashewa.
2.     Mu zauna cikin shiri abin da ka iya biyowa bayan wannan lokaci na bakin ciki da zaman makoki. Fushi da zargin juna za su biyo baya, kuma mu Musulmi ne za a fi cutarwa. Tuni an kakkama Musulmin da ba su da laifi ana musguna musu ana cutar da su ana kai musu hari ana wulakanta su, an kai farmaki ga masallatai da makarantun Musulunci da dama.  Don haka ya kamata kafafen watsa labarai da jami’an tsaro da coci-coci da sauran hukumomi su yi taka-tsantsan kada su musguna ko su yi kudin goro ga daukacin al’ummar Musulmi. Mu kuma a namu gefen mu yi namu kokarin. Kuma mu fito da karfin murya mu la’anci wannan mugun ta’addanci. Kuma wajibi ne mu rika ziyartar asibiti muna ba da taimakon jini mu rika rubuce-rubuce a jaridu kan illar haka mu bayyana matsayinmu a fili. Alhamdu lillahi, wata sabuwar kungiyar yaki da nuna kyama da bambanci ga Musulmi, wato Forum Against Islamophobia and Racism (FAIR), ta bude shafin intanet kuma tana gudanar da bincike kan duk hare-haren da aka kai wa Musulmi. Suna bayar da bayanai ga ’yan sanda, sai dai suna fama da karancin kudi don haka sun bukaci mu roke ku ku tallafa musu, don su ci gaba da gudanar da aikinsu.
3.    Na uku, wajibi ne mu samar da ingantaccen shugabanci a tsakanin al’ummarmu. Akwai bukatar masu gudanar da masallatanmu ya zamo sun san yadda za su warware matsalolin addininmu da na rayuwarmu da bukatun iliminmu. Bai kamata kwamitocin masallatanmu su ci gaba da kasancewa kamar kulob na Musulmin da suka yi ritaya daga aiki ba. Al’ummarmu tana da wadatar mutane masu hazaka da kuma dukiya. Ya wajaba a yi amfani da wadannan domin amfaninmu.
4.    Ya wajaba Musulmi su fahimci cewa neman ilimi da koyo abu ne da ked a dogon zango, a gidajenmu mu ci gaba da koyon ilimi don inganta rayuwarmu. Wajibi ne mu zama mazaje nagari da mata nagari, iyaye masu wayewa da ’ya’ya masu godiya. Manyan dabi’unmu na adalci da tausayi wajibi ne su karu a tsakaninmu da sauran jama’a a cikin dukkan al’amura, ga iyalanmu da al’ummarmu da kuma kasarmu. Kuma daga nan ne kyawawan dabi’un adalci da tausayi za su watsu a sauran kasashen duniya. Idan muka san abin da ya kamata mu yi, za mu kintsu kuma mu taimaki saura wajen gina al’umma da kasa. Kuma hakan zai fara ne daga daidaikunmu. Wannan hanya ta gina lafiyayyiyar al’umma mai tsaka-tsaki mai cike da daidakun mutane adalai Alkur’ani ya bayyana tad a “Ummatan wastan” wato “Al’umma matsakaiciya.” Kuma kamar yadda na fada a hudubar da ta gabata, ginshikin samun lafiyayyiyar al’umma matsakaiciya shi ne zuciyar taimakekeniya. Idan muka sanya Allah a zukatanmu za mu samu natsuwa ‘sakina’  da kwanciyar hankali da tausayin juna. Wajibi ne koyaushe mu sanya Allah a zukatanmu, mu tuna gafala ba namu ba ne.
Shekarun farko na Musulunci a Makka kafin Hijira zamani ne da ke cike da kunci. An musguna wa Musulmi an ci zarafinsu kuma sun mutu saboda sun yi imani da Allah. Amma za ku ga surorin farko na Alkur’ani Mai girma sun fi mayar da hankali ne kan gina kyawawan dabi’u da tsarkake zuciya. Wannan babban mataki ne na kintsawa ta yadda Musulmi za su iya fuskantar manyan kalubalen da ke zuwa da fadada da samun nasara. Don haka Makka wadda take cike da makiyayan dabbobi ake ganin gidadawa ne ta sauya zuwa jagorar wayewa da ci gaba a duniya, kamar yadda maeri yake iya tace baki karfe daga zinare.
’Yan uwa maza da mata! Mu dauki halin kunci da hadarin da muke ciki ya zamo kamar na mutanen Makka, ta yadda za mu yi wankan tsarki ga al’ummarmu, mu kyautata kawunanmu mu zama al’umma matsakaiciya da Allah Yake so mu kasance. Magabatanmu na kwarai ba su cika damuwa damuwa da zahiri ba fiye da badini. Yayin da duniyarmu ke fashewa a kanmu, yanzu ba lokaci ba ne na tsayawa muna ta surutu kan dogon gemu ko fasalin suturarmu ba, (duk da cewa su ma bangare ne na Musulunci). Sahabban Annabi (SAW) ba su cika damuwa da tufafin da suka sanya ba, sai dai abin da ke cikin zukatansu.

Imam Murtada Gusau ya gabatar da wannan huduba ce a ranar Juma’a 7 ga Ramadan 1435 BH daidai da 4 ga Yuli, kuma za a iya samunsa a 08038289761 ko [email protected]