Ina son likita ya taimaka mini da ire-iren kalar abinci masu suga da marasa suga?
Daga Yusuf Hassan, kaura
Amsa: Ai Malam Yusuf ka debo da yawa. Kusan abinci kalilan ne fa ba su da suga, su ma din kuma idan suka shiga jini sai an mai da su suga. Watakila daga mai (maiko) sai nama sai kifi, su ne ba su da suga kafin a ci.
Da fari ya kamata ka san mene ne ma suga. Domin sai ka fahimci mene ne suga sannan za ka san nau’ukan abinci kadan ne ba su da suga. Suga a kimiyyance ya kunshi sinadarai kala shida; akwai glucose, fructose, galactose, sucrose, maltose, da lactose. Duk wani nau’in suga da ka taba ci dayan wadannan ne. Shi suga da ka sani na shan kunu ko shayi shi ne sucrose, wanda ake tatsa a rake. Sauran ‘ya’yan itatuwa su ma suna da nasu irin sugan wanda dole daya ne daga cikin wadannan da aka lissafa. Haka ma hatsi da sauran kayan abinci, duk suna da sukari. Kai har irinsu madara da yagot da kake gani kake ji kamar ba zaki, suna da sukari wanda shi ne lactose, wanda ka ga shi ma daya ne daga cikin wadancan da aka lissafa.
Wani abin da watakila sai ka kara la’akari da shi game da su wadancan abinci da ba su da suga wato nama, kifi da maiko, idan fa suka shiga jiki su ma ana mayar da su suga ne kafin jiki ya yi amfani da su. Wannan nau’in suga da ake mayar da su shi ne glucose, wanda shi ma ka ga daya ne daga cikin wadannan nau’in suga da aka lissafa. Ke nan jiki ba zai iya rayuwa ba suga ba. Sai dai a ce jiki na bukatarsa daidai misali. Idan ya yi yawa a jini tara shi ake a sauya shi har ila yau zuwa kitse, inda za a tara shi a teba ko a damtse ko a cinya da sauran wuraren da jiki ke ajiyarsa, sai bukatarsa ta tashi. Bukatar tana tashi ne kuwa yayin jin wata yunwa, kamar lokacin azumi, ko yayin motsa jiki inda har-ila-yau za a sake narka kitsen su koma suga. To ka ji fa labarin suga.
Ko me ke sa saurin jin yunwa? Ni da na ci abinci bayan awa daya zuwa awa daya da rabi sai yunwa ko me ke sa hakan?
Daga Alhaji Jinjiri, Lagos
Amsa: Da ma abinci musamman masu kara kuzari awa daya zuwa awa daya da rabi suke yi a ciki tun daga tumbi zuwa hanji kafin a tsotse su. Abinci masu gina jiki sune wadanda a wasu lokuta sukan kai awanni uku zuwa hudu. To ka ga kenan idan abincin mutum ya kunshi gayan kayan kara kuzari ne kawai, ba masu gina jiki kamar nama ko kifi – abin da Hausawa ke cewa lami, to tabbas nan da nan wata sabuwar yunwa za ta sake kama shi.
Na kan ga wani abu na motsi a damtsena. Idan na duba sai in ga wurin yana rawa kamar akwai wani abu a ciki amma ba zafi. Ko mene ne hakan?
Daga Ibrahim Katsina
Amsa: E, haka nan kawai a wasu mutane naman jiki zai iya kama rawa shi kadai. A wasu lokutan da zafi, a wasu lokutan kuma ba zafi. Ba ciwo ba ne ba kuma matsala ba ce, don haka ba abinda ya kamata a yi wa wurin sai dai a zura ma sarautar Allah ido. Sai dai idan mai zogi ne, shi ne ake neman maganin zogi na sha ko na fesawa, irin wanda ka ga ana fesawa ‘yan wasa idan sun samu irin wannan. Wuraren da akan ga tsokar jiki na irin wannan rawa a jikinmu sun hada da damtse, da tika-tiki wato bayan gwiwa, da gira.
Duk da haka wasu masana suna ganin akwai rashin wasu sinadarai a jiki da za su iya sa yawan hakan, wanda wasu daga cikinsu shi ne sinadarin magnesium wanda akan samu a gyada da ayaba da alaiyahu, wadanda idan ba a ci daya daga cikinsu a rana ba, za a iya yawan samun matsalar.
Wai me ya sa wasu mutane har da ni, ba ma iya cin yaji ne, da na ci zan ji kirjina yana mini zafi sosai. Ko alamar wani ciwo ne hakan?
Daga Hassana, Kaduna
Amsa: Abin da hakan ke nufi shi ne bangon cikinku wato bangon tumbin ciki ba ya son yaji. Don haka da kai da masu samun irin wannan sai ku guje shi, domin idan ba ku bari ba zai iya jawo muku gyambon olsa. Amma mu da namu yake zama lafiya ko mun ci barkono za mu iya ci duk lokacin da muka ga dama.
Maras lafiya ne mai ciwon olsa, amma yanzu olsar ta warke sai dai yawan shakuwa. Ko me ya kamata a yi?
Daga Musa Ahmad
Amsa: Da fatan dai an yi hoton ciki na kyamara ya bayyana cewa akwai olsa, ba haka nan kawai yake shan magungunan olsa ba. Idan aka yi hoton ciki ya tabbata olsa ce akwai ka’idar watannin da ake shan magunguna, dole sai an bi su za ta tafi. Idan har yanzu mai olsa na yawan shakuwa bai warke ba kenan, domin yawan shakuwar ma alama ce ta ciwon olsa.
Ni kuma idan na sha kayan marmari masu tsami kamar lemo ko abarba sai kuraje sun fito mini a harshe. Ko mene ne abin yi?
Daga Nasiru Shehu, Sokoto
Amsa: Shike nan sai ka guji ‘ya’yan itatuwa masu tsami, sai ka samu lafiya. Wani nau’in acid ne (citric acid) wanda ake samu sosai a ‘ya’yan itatuwa masu tsami ke kona maka harshe, amma sinadarin ragagge ne a wadanda suka nuna sosai.
Bayan yawan shan ruwa akwai wani abu da ya kamata wanda aka ce yana da tsakuwa a mafitsara ya rika yi?
Daga Maman Sadik, Gombe
Amsa: Wanda aka cewa yana da tsakuwa a mafitsara ko a matsarmama bayan yawan shan ruwa ana so ya rage cin maiko da rage yawan shan shayi, da rage yawan cin jan nama da alaiyahu, wadanda sinadaransu ne ke taruwa su zama tsakuwa a mafitsarar da matsarmama. Sa’annan idan aka yi wadannan aka ga abin ba sauki yana da kyau a rika yawan komawa likita, domin wasu watakila sai an yi tiyata an cire, wasu kuma da kansu suke gangarewa ko zagwanyewa.