✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ta watsar da aikin sakatariya domin gyaran takalmi

Wata matashiya mai Misis Sophia Amaka, ta ajiye aikinta na sakatariya domin ta zama mai hada wa da kuma gyaran takalmi. Mai kimanin shekaru 26…

Wata matashiya mai Misis Sophia Amaka, ta ajiye aikinta na sakatariya domin ta zama mai hada wa da kuma gyaran takalmi.

Mai kimanin shekaru 26 a duniya, matar ta ce ta dauki matakin ne domin cikar burinta a rayuwa na zama mai hada takalmi.

Ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) cewa ta yanke shawarar sadaukar da aikin nata tun shekarar 2016 domin ta fara sana’ar hada takalmin.

A cewarta, tana samun isasshen lokacin kanta, kuma tana samun kudin da babu wani aikin da zai kawo mata kwatakwacinsu ta sanadin sana’ar hada takalmin.

“Na shiga sana’ar ne domin ina son in bambanta da kowa, kuma na yi abin da ya sha bamban da kowacce mace,” inji ta.

Ta ce sai da ’yan uwanta suka yi mata dariya lokacin da ta sanar da su shirin nata.

“Shin ba ki ganin akwai wasu sana’o’in na daban da ya kamata ki yi a maimakon hada takalmi?. Ko dai so kike ki kunyata mu ne?” kamar yadda suka ce da ita.

Sai dai a daya gefen kuma, ta bayyana cewa wadansu mutanen na gefe sun karfafa mata gwiwar ta dage kan abin da take da sha’awar yi, kuma zuwa yanzu babu wanda ya sake yi mata gani-gani.

“Na fara ganin yadda ake hada takalmi a majami’ar RCCG da ke Kubwa a Abuja.

“Lokacin majami’ar tana gudanar da taron  shekara-shekara na koyar da sana’o’i da kasuwanci  a 2016.

“Babbar nasarata a yanzu ita ce bayanan da nake samu daga kwastomomina. Na kan hada takalmi sawu-ciki da kuma mai yatsu, kuma ina gyara takalmin maza da mata.

“Hada takalmin da gyaransu yana ba ni sha’awa,” a cewarta.

Ta ce ta zabi sana’ar saboda wata rana shagon nata zai bunkasa.

Ta kara da cewa tana da masu koyon sana’ar da dama wadanda ta koya wa, kuma har sun fara hada wa kwastomominta takalmi masu igiya (sandal).

Misis Amaka, wacce ta yi kira ga ’yan mata da su nemi abin yi, ta ce tana son zo wajenta domin ta koya musu sana’ar hada takalmin.

“Kawai mutum ya bi abin da zuciyarsa take so, ko ta halin kaka ne kada ka saurari ra’ayin jama’a.

“Yin abin da ranka ke so yana da matukar muhimmanci kuma wannan ne ya sa nake ci gaba da samun nasara.

“Son da nake yi wa sana’ar shi ne kashin bayan jin dadina, ina kuma fatan kara samun horo a kai domin in zama ba ni da na biyu,” inji ta.