’Yan sanda a Jihar Bauchi sun kama wata matar aure da ta hada baki da ’yar uwarta suka watsa wa budurwa mijinta ruwan zafi a fuska.
Kakakin ’yan sanda jihar, SP Ahmed Wakil ya ce sai da wadanda ake zargin suka lakada mata duka, sannan suka zuba mata ruwan zafi, wanda hakan ya jawo mata munanan raunuka a wuyanta da kuma kuncinta.
- Kano: Abba ya rushe shataletalen gidan gwamnati
- DAGA LARABA: Yadda Kungiyoyin NGO Ke Neman Hana Zaman Aure A Maiduguri
Sanarwar da ya fitar a ranar Talata ta cea wadanda ake zargin su ne Fatima Muhammad-Sani mai shekara 17 tare da ’yar uwarta Zulaihat Muhammad-Sani.
Kazalika, ya ce tuni aka garzaya da matashiyar da akka kina da ruwan zafin zuwa asibiti domin kula da lafiyarta.
Ita kuwa matar auren da ’yar uwarta sune tsare a yayin da ake ci gaba da bincike.