Wata mata ta tura ’yar kishiyarta, mai shekara 14 da ke zaune a unguwar Linde a Karamar Hukumar Girei a Jihar Adamawa zuwa gidan yari.
Aminiya ta ruwaito cewa mahaifiyar yarinayr mai suna Zainab, Halima ta samu saɓani da ita a ranar 26 ga watan Maris, 2024.
Duk da cewa ta sa wasu mutane sun yi mata dukan tsiya, sai ta yanke shawarar yin hulɗa da Zainab kuma ta jajirce wajen ganin kada kowa ya kuɓutar da ita.
A ranar 26 ga watan Maris, ta nemi kotun Majistare ta Vinikilang ta tura yarinyar zuwa gidan yari.
Ba tare da ɓata lokaci ba, alƙali ya yanke wa yarinyar hukuncin zaman gidan yari.
Alƙalin kotun, Ibrahim Zira Yerwa, ya yanke hukuncin ne da misalin ƙarfe 4:00 na yammacin ranar Alhamis, kuma an aika da Zainab zuwa gidan gyaran hali na Yolde Pate da ke Karamar Hukumar Yola ta Kudu a ranar 28 ga watan Maris 2024.
’Yan uwan yarinyar sun ruwaito cewa ta yi buɗa baki ne a gidan gyaran hali na Yolde Pate ranar Alhamis.
‘Yan uwan Zainab na neman Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri da ya kai musu dauki kan lamarin.
“Yau ranar hutu ce kuma ƙarshen mako ya zo, hakan na nufin ba za a yi wani aiki ba, muna kira ga Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri da ya sa baki cikin gaggawa kan wannan zaluncin domin Zainab ba ta kai shekara 18 ba,” in ji su.
Wannan lamari dai ya tayar da hankulan al’ummar yankin, inda suke kira da a tabbatar da adalci, a kuma saki Zainab daga gidan yari.