✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta sheka mata tafasasshen ruwa kan kawo gulmar mijinta mijinta

Rundunar ‘Yan sandan Jihar Kano ta gurfanar da wata matar aure mai suna Hassana Rabi’u a gaban Kotun Lardi ta Shari’ar Musulunci da ke Rijiyar…

Rundunar ‘Yan sandan Jihar Kano ta gurfanar da wata matar aure mai suna Hassana Rabi’u a gaban Kotun Lardi ta Shari’ar Musulunci da ke Rijiyar Lemo kan zarginta da sheka wa wata makwabciyarta ruwan zafi don huce haushin tsegunta mata labarin mijinta yana neman wata budurwa a unguwar.
Takardar karar ta bayyana cewa Hassana Rabi’u ta sheka wa makwabciyarta mai suna Hassana Salihu tafasasshen ruwan ne a daidai lokacin da ake kokarin tabbatar da gaskiyar labarin da makwabciyar tata ta gaya mata cewa mjinta mai suna Malam Rabi’u yana sumbatar budurwar a wani zaure. A cewar takardar karar “Lokacin da mijin  Hassana Rabi’u ya dawo gida sai ta tunkare shi da wannan tsegumi da makwabciyarta ta gaya mata, a take mijin nata ya kira mijin makwabciyar a waya, lamarin da ya sa suka hadu a wuri guda don kure mai karya. A wanann lokaci ne ita ma budurwar ta tabbatar da cewa Malam Rabi’un ya kebe da ita. A daidai wannan lokaci ne ita kuma wacce ake zargin Hassana Rabi’u da takaici ya kama ta sai ta dauko wani ruwa da ke tafasa a kan wuta ta sheka wa Hassana Salihu a kirji lamarin da ya janyo kirjinta ya sabule.”
Alkalin Kotun Mai shari’a Halhalatul-Huza’i Zakariyya ya bayar da umarnin sakaya wacce ake zargin a gidan maza tare da dage shari’ar.