Wata mata mai suna Esther Mba, ta rasa ranta a yayin tirmitsitsin dasa wasa kan kayan tallafin Covid-19 a ma’ajiyar karamar hukumar Kaura da ke garin Kagoro a daren Litinin.
Matasan da suka ba da shaida sun ce sun fasa ma’ajiyar ne da misalin karfe 7 na dare yayin da suka bijire wa harbin ‘yan sanda da na ‘yan banga a kokarin tarwatsa su, inda su kayi nasarar kutsawa tare da yin awon gaba da duk kayayyakin da aka ajiye a ciki.
- #EndSARS: Rarara ya saka kyautar Motoci da kudade a gasar Mawaka kan zaman lafiya
- Fadar Shugaban Kasa ta kafa kwamitin Gwamnoni 6 don inganta rayuwar matasa
Yayin da ya ke tabbatar da faruwar lamarin, Sakataren Karamar Hukumar Kaura, Mista Sunday Tibishi, ya ce babu wanda jami’an tsaro su kayi nasarar cafke wa a yayin wawason abincin.
Aminiya ta ruwaito cewa, Gwamnatin Jihar Kaduna ta sassauta dokar hana fita ta awa 24 da ta shimfida a kokarinta na dakile yunkurin mutane na dasa wawa a kan rumbunan ajiyar abinci.
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar, Samuel Aruwan ne ya sanar da hakan a ranar Litinin da cewa sabuwar dokar hana fita wadda za ta fara aiki daga yau Talata za ta fara ne da karfe 4:00 na Yamma zuwa 6:00 na safe.
Sai dai Kwamishinan ya ce ba a yi sassauci a kananan Hukumomin Kaduna ta Kudu da Chikun ba, inda ya ce dokar tana nan daram ta awa 24 kamar yadda aka shimfida a baya.