Wata mawakiya mai suna Brianna Mary Shihadeh mai sha’awar gyaran jiki wadda ta raba harshenta biyu ta bayyana yadda za ta iya dandana abubuwa biyu daban-daban a lokaci guda.
Hakan dai ya sa mutane suka yi mamakin irin fasaharta wajen bambance dandano da harshenta da ta raba.
- Gwamnati za ta kafa kamfanin sarrafa nama a Yobe
- ’Yan Boko Haram sun yi wa ’yan jari-bola 20 yankan rago a Borno
A kwanakin nan ta bar mutane cikin mamaki bayan ta dandana ruwan lemon biyu a lokaci guda, inda ta sa rabin harshenta a cikin kowane kofin gilashi.
Bayan da aka wallafa bidiyon Brianna Manhajar TikTok wanda ya dauki hankalin jama’a sosai, Brianna, wacce ke zaune a Kudancin Jihar Kalifoniya a Amurka, bidiyonta ya samu sharhi da ra’ayoyin mutum 293,000, tare da sanya mabiyanta farin ciki.
A cikin dan lokaci idan an yi la’akari da ra’ayin jama’a game da muhawarar da dandana lemon Pepsi da Koka-Kola, Brianna ta yi, watakila ya zama abu mai rikitarwa, inda ta tabbatar da cewa, ‘za ta iya dandana bambanci tsakaninsu lokaci guda.
Brianna – wacce ke da adireshin @flowerfriendly ta gudanar da gwajin dandanon gishiri da zaki, inda ta raba harshenta a tsakanin gilasan ruwan sukari daya da wani mai dauke da ruwan gishiri.
Da take waiwayar irin wannan haduwar dandanon, Brianna ta ce, a bar kwakwalwarta haka ba ta cikin rudani. An bar masu amfani da TikTok cikin mamaki bayan sun shaida kwarewar Brianna da ba kasafai ba ne ake iya samun hakan, wasu sun yaba bidiyonta da cewa ya kasance “mai gamsarwa.”
Wani mutum ya ce: “Ban taba tunanin yin amfani da wannan ba! Kina da ban-mamaki. Ba zan iya daina kallo ba.”
Wani ya ce: “Wannan shi ne abin da nake bukata. Tambayoyi da yawa a wannan duniyar kuma babu wanda ke tambayar wadanda suka dace zuwa yanzu.”
Brianna, wacce wani lokaci ana kiran ta da Flower, tana da fuska mai ado da zanen tattoo da yawa da huda iri-iri a jikinta.