✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ta kona ’yar aikinta da ruwan zafi

Wata yarinya ’yar shekara 9 da ke aikin baranta, wato wanke-wanke, debo ruwa da shara, ta gamu da fushin uwar dakinta wacce ta watsa mata…

Wata yarinya ’yar shekara 9 da ke aikin baranta, wato wanke-wanke, debo ruwa da shara, ta gamu da fushin uwar dakinta wacce ta watsa mata tafasasshen ruwa, wanda ya yi sanadiyyar konewar jikinta.
Yarinyar mai suna Chinwedu Precious, wacce a yanzu take samun kulawa a wani asibiti mai zaman kansa na Rems-Yems, ta gamu da wannan ibtila’in ne a gidan da take aiki, wanda yake a Unguwar Alagbado a Legas.
Matar wadda ta yi aika-aikar, ’yar shekara 26 mai suna Ifeoma Mbakwe, ’yar asalin Jihar Anambara ce da ke zaune a Unguwar Alagbado, matasan anguwar ne suka kame ta bayan da ta kwarara wa ’yar aikin nata tafasasshen ruwa; suka kuma damka ta ga hukumar ’yan sanda. Kuma a yanzu an gabatar da ita a gaban kuliya.
Wata makwabciyar gidan da abin ya faru, mai suna Joy Sunday, wadda ta bayyana takaicinta bisa lamarin, ta ce abin da Ifeoma ta yi, ya yi muni kwarai; ya kuma keta alfarmar ’ya mace. Ta yi kuma kira ga mahukunta da su tabbatar an hukunta ta, don hakan ya zamo izna ga na gaba.