✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta kashe mijinta bayan ya kama ta da kwarto a cikin gidansa

Ya mutu ne saboda caka masa wuka da ta yi a cikinsa, lokacin da ya kama ta da kwarton.

Ana zargin wata mata da caka wa mijinta, mai suna Abdullatif, wuka har sai da ya ce ga garinku nan bayan ya kama ta tana lalata da wani kwarto a cikin gidansu na aure.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:00 na daren ranar Lahadi a unguwar Jattu da ke Karamar Hukumar Etsako ta Yamma a Jihar Edo.

Lamarin ya faru ne lokacin Abdullatif ya dawo ya sameta tare da mutumin a cikin dakinsu.

Wata majiya mai tushe ta ce, “A baya, mijin yana da mata biyu a gidan, amma tilas ta sa ya fita ya kama wa uwar gidansa haya a wata unguwar don a samu zaman lafiya, inda ya kyale ita amaryar a nan gidan.

“Ya kan raba musu kwanaki, amma akwai zargin da ake yi cewa ta kan kawo kwarto a duk lokacin da yake da kwana a gidan uwar gidan.

“Kwatsam kuwa ran nan sai ya shigo gidan cikin dare inda ya ritsa ta tare da kwarton a cikin dakinsa.

“A nan ne ya yi yunkurin kama kwarton, inda a sakamakon haka, matar tasa ta caka masa wuka sau biyu a cikinsa, domin ta ba kwarton damar tserewa, alabasshi ta ce fashi aka zo yi musu har aka ji masa rauni.

“A sakamakon hakan, ko kafin a kawo masa dauki ya riga ya mutu. Zuwan ’yan sanda ne ma ya hana ’yan unguwar da suka fusata su kashe matar,” inji majiyar.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, Bello Kongtons ya ce tuni jami’ansu suka cafke matar.