Wata mata mai shekara 42 mai suna Temitope Akinola, da ke zaune a garin Shagamu a jihar Ogun, ta shiga komar ‘yan sanda bayan da ta bai wa jikanta mai kwanaki biyu a duniya maganin kwari gubar sinifa lamarin da ya yi sanadiyar mutuwarsa.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Ogun DSP Abimbola Oyeyemi, ya shaidawa Aminiya cewar matar ta tabbatar masu da cewa, ta kashe jikan nata ne saboda kiyayyar da take wa ubansa domin bata so ya auri ‘yar ta inda tayi yunkurin zubar da cikin da ‘yar tata ta samu tun daga fari amma limamin cocin da take zuwa ya hanata.
“Sai ta hakura har ‘yarta haife yaron, ta kashe shi ne a lokacin da mahaifiyarsa ta kwantar da shi ta nufi bandakin wanka, yanzu haka tana hannun hukuma an kuma kai gawar jaririn dakin ajiyar gawa na asibitin koyarwa na jami’ar Olabisi Onibanjo, domin gudanar da bincike.” in ji DSP Abimbola Oyeyemi.