✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta haifi ’yan 6 bayan shekara 27 da aure

Doris wadda ta fito daga kauyen Koluama da ke Karamar Hukumar Ijaw ta Kudu a Jihar Bayelsa, ta ce sun yi aure da mijinta tun…

Wata mata mai suna Doris Levi Wilson ta haifi ’yan shida da aka sanya wa suna Miracle da Mercy da Merit da Marvis, dukansu mata sai Marvellous da Mirabel su biyun maza bayan shekara 27 da aurenta da mijinta.

Doris wadda ta fito daga kauyen Koluama da ke Karamar Hukumar Ijaw ta Kudu a Jihar Bayelsa, ta ce sun yi aure da mijinta tun 1994 ba tare da sun samu haihuwa.

An haifi ’yan shidan ne a ranar 9 ga Fabrairun nan, kuma dukkansu suna cikin koshin lafiya.

Mahaifiyar ta shaida wa Aminiya cewa “Na yi matukar farin ciki da na haihu lafiya na gode wa Allah cikin ikonSa Ya ba ni ’ya’ya shida na haife su lafiya.”

Da Aminiya ta tuntubi mahaifin ’yan shidan, Mista Levi Wilson kan wannan karuwa, sai ya ce, “Wannan wata baiwa ce daga Allah, yau na kasance cike da farin ciki, kuma yadda Allah Ya ba ni su Shi zai ba ni ikon kula da su.”