✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…Ta dauki masu juna biyu 1,700 zuwa asibiti kyauta a Jihar Nasarawa

Kungiyar Direbobi ta Kasa (NURTW), reshin Jihar Nasarawa ta ce cikin shekara biyu ta dauki mata masu juna biyu su 1,700 zuwa asibitoci kyauta. Shugaban…

Kungiyar Direbobi ta Kasa (NURTW), reshin Jihar Nasarawa ta ce cikin shekara biyu ta dauki mata masu juna biyu su 1,700 zuwa asibitoci kyauta.

Shugaban Kungiyar NURTW ta Jihar, Alhaji Salihu Adamu, ya bayyana haka a jawabinsa a wajen babban taron kungiyar karo na 7 da aka gudanar a otel din Ta’al da ke Lafiya babban birnin jihar. Ya ce, wannan shiri na musamman wanda kungiyar ke gudanarwa da hadin gwiwar Kungiyar Emergency Transport Scheme kawo yanzu an aiwatar da shirin a kananan hukumomin Nasarawa-Eggon da Doma da Kokona da Obi da Wamba da sauransu inda ya ce wadansu direbobin kungiyar da dama a wadannan kananan hukumomi ke daukar nauyin kai masu juna biyun musamman daga yankunan karkara zuwa asibitoci kyauta don haihuwa da sauransu.

Ya ce shirin yana daga cikin gudunmawar da kungiyar ke bayarwa ne wajen rage matsalolin da masu juna biyu da ke yankunan karkarar jihar ke fuskanta a lokutan nakuda da suke sanadiyar barin ciki da sauransu. Ya ce, “Wadannan direbobin sa-kai  ’ya’yan kungiyarmu mun horar da su ne na wasu watanni ta yadda za su tuka masu juna biyu zuwa asibiti don samun kula ba tare da an samu matsala ba,” inji shi.

Shugaban ya bukaci a yi wa manyan hanyoyin jihar gyara tare da gina sababbi don tabbatar da dorewar shirin a fadin jihar da saukaka  wa jama’a harkar safara a jihar da kasa baki daya.

Ya ce kyan hanya na saukaka tafiya da daukar wadannan mata masu juna biyu da kayayyaki kuma ya rage kuncin rayuwa da sauransu.

Abubuwan da aka gudanar a wajen taron na shekara-shekara sun hada da zabe da kaddamar da sababbin shugabannin kungiyar a jihar inda Shugaban Kungiya, Alhaji Salihu Adamu da Sakatarensa Abubakar Maikanti da Ma’aji Saleh Danmusa  da sauran shugabanni, suka samu amincewar mambobin kungiyar a jihar kan su cigaba da ja ragamar shugabancin kungiyar a jihar ba tare da hammaya a zaben ba.