✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Super Eagles za ta yi wasan sada zumunta da Ingila

Sakatare Janar na Hukumar NFF Mohammed Sanusi ya bayar da sanarwar kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles za ta yi wasan sada zumunta da Ingila.…

Sakatare Janar na Hukumar NFF Mohammed Sanusi ya bayar da sanarwar kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles za ta yi wasan sada zumunta da Ingila.

Sanusi ya ce ana sa ran wasan zai gudana ne a watan Yunin 2018 wato ana gab da fara gasar cin kofin duniya, amma kawo yanzu ba a sanar da wuri da kuma takamaiman ranar da wasan zai gudana ba.

Ya ce wannan wasa tamkar gwajin dafi ne a kokarin tunkarar Gasar Cin Kofin Duniya da kasashen biyu suke ciki, inda kowaccensu za ta halarci gasar a Rasha a badi idan Allah Ya kaimu.

Rabon da kasashen biyu su hadu a wasan sada zumunta tun a watan Nuwamban 1995 a filin wasa na Wembley da ke Ingila kuma Ingila ce ta doke Najeriya da ci daya mai ban haushi.

Idan za a tuna Najeriya dai ta lallasa Ajantina da ci 4-2 a wasan sada zumuntar da suka yi a Rasha a kwanakin baya.

Najeriya za ta fafata a gasar cin kofin duniya ne a rukunin D da kasashen Ajantina da Kuroshiya da Iceland, yayin da Ingila kuma tana rukunin G ne da kasashen Beljiyam da Panama da kuma Tunisiya.