Mahmud, babban dan mutumin da ya kafa kungiyar ISWAP, Mamman Nur Albarnawy, ya mika kansa ga jami’an tsaron Sibil Difens a Maiduguri, Jihar Borno.
Mahmud mai shekaru 22, ya mika wuya a ne ranar Lahadi, 12 ga watan Mayu da muke ciki.
Wata majiyar leken asiri ta shaida wa Zagazola Makama, kwararre kan yaki da ta’addanci a tafkin Chadi, cewa an tabbatar da cewa Mahmud ne babban dan Mamman Nur Albarnawyshi ne bayan an yi masa binciken kwakwaf a hedikwatar Sibil Difens (NSCDC) da ke Maiduguri.
Majiyar ta ce jami’an rundunar sun taimaka masa ne ta hannun kawunsa da ke Gamborun Ngala bayan samun labarin cewa yana son mika wuya ga gwamnati a hukumance.
An aika wani amintaccen wakili ya kai shi Maiduguri yadda suka isa Maiduguri ne a ranar 11 ga watan Mayu da misalin karfe 1 na rana.
Daga bisani wani jami’in leken asiri na rundunar ne ya bayyana cewa Mahmud ya fice daga sansanin Ali Ngulde da ke tsaunin Mandara a karamar hukumar Gwoza zuwa Maiduguri inda ya yi kusan wata guda a Gwange kafin ya koma Gamboru Ngala ba tare da alamun damuwa daga al’ummomi ba.
A lokacin da yake zamansa a Gamboru Ngala, wasu daga cikin masu biyayya ga mahaifinsa sun bukaci ya koma yankin tafkin Chadi domin yin mubaya’a ga kungiyar ISWAP, amma ya ki, saboda cin amana da kuma kashe mahaifinsa da aka yi.
Ya amsa laifin kai hare-hare a Bama, Banki, Gwoza da wasu wurare da dama a matsayinsa na matsakaicin mayaki a karkashin kungiyar Boko Haram a baya.
An mika Mahmud ga wurin gyaran hali na Bulunkutu don ci gaba da ba da bayanai da kuma tsare shi.
Wanene Mamman Nur?
A shekarar 2013, an tilasta wa manyan kwamandojin marigayi Muhammad Yusuf, wanda ya kafa kungiyar Boko Haram, wadanda suka hada da Mamman Nur, Khalid Albarnawi, Abubakar Shekau, Kaka Ali, Mustapha Chad, Abu Maryam da Abu Krimima, barin Maiduguri, bayan tsanantar kai hare-hare daga jami’an tsaron hadin gwiwa a Maiduguri da nufin cafko su.
Bayan wani lokaci sai suka sake haduwa a dajin Sambisa inda suka ci gaba da kai hare-hare a garuruwa da kauyuka, inda suka kafa kungiyar ta zama kungiyar ta’addanci.
A watan Maris din 2015 ne Boko Haram suka yi mubaya’a ga Halifancin Abubakar Al-Baghdadi na ISIS.
Kungiyar ISIS ta amince da mubaya’ar ta kuma bayyana Abubakar Shekau a matsayin Wali na farko na kungiyar ISWAP.
Daga baya kungiyar ISIS ta tsige Shekau bayan da Mamman Nur da Abu Mussab Albarawi, wadanda ’yan majalisar tuntubar Shura ne suka shigar da kara a kan shugabancinsa.
A wancan lokacin ana zargin Marigayi Shekau da tsattsauran ra’ayi wajen yin kisa ba bisa shari’a ba, rashin adalci, rashin kwarewar shugabanci da kuma kashe mata da kananan yara haka siddan.
Rikicin cikin gida ya haifar da rabuwar kungiyar Boko Haram da ISWAP, wadanda suka koma yankin tafkin Chadi. na Marte da Abadam don kafa halifancinsu tare da Mamman Nur a matsayin sabon Shugaban Kungiyar ISWAP a wancan lokacin.
A ranar 21 ga watan Agustan 2018, ne aka Kashe Mamman Nur a wani harin da Abou Mossab Albarnawyy ya jagoranta tare da wasu mayakan ISWAP.
Wata majiya ta ce an kashe Nur ne saboda sakin daliban Sakandaren ’yan mata na Dapchi, ba tare da neman kudin fansa daga gwamnatin Najeriya ba.
Majiyar ta kara da cewar Kashe Mamman Nur, ya haifar da zaman Abou-Mossab Albarnawyy a matsayin jagoran ISWAP.