Dan kwallon gaba a kungiyar Super Eagles Eammnuel Emenike ya bayar da tabbacin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles za ta haye gasar cin kofin duniya da zai gudana a Brazil a shekara mai zuwa.
Sai dai dan kwallon ya janyo hankalin takwarorinsa da cewa kada su kuskura su raina duk kasar da za a hada su a a gasar neman gurbin zuwa gasar cin kofin duniya a mataki na karshe (Play-Offs) da za a yi a tsakiyar watan Oktoba mai zuwa da kuma tsakiyar Nuwamban 2013 don tantance kasashe biyar da za su wakilci Nahiyar Afirka a Brazil.
Najeriya dai ta samu nasarar hayewa matakin karshe na neman zuwa gasar cin kofin duniya ne bayan ta samu nasara a kan Malawi da ci 2-0 a garin Kalaba a makon jiya.
Sauran kasashe tara da suka haye kuma suke jira a raba su da abokan karawarsu a jadawalin da Hukumar shirya kwallon kafa ta Afirka (CAF) za ta gudanar a Cairo da ke Masar a ranar Litinin mai zuwa sun hada da Kwaddebuwa da Aljeriya da Masar da Kamaru da Ghana da Burkina Faso da Cape berde da Senegal da kuma Etopiya.
Sai dai akwai yiwuwar Najeriya ba za ta hadu da kasashen Kwaddebuwa da Ghana da Aljeriya da kuma Cape berde ba, don an kasa su a rukuni daya ne.
Amma akwai yiwuwar Super Eagles ta hadu da Senagal ko Burkina Faso ko Kamaru ko Etopiya ko Masar a jadawalin da ake sa ran fitarwa.
Emenike ya ce idan aka lura, za a ga cewa babu wata kasa da ta kai wannan mataki wacce ba ta cancanci kaiwa ba, don haka kada takwarorinsa su dauka sun riga sun haye gasar cin kofin duniya a wannan lokaci.
“karamar kasa da ka raina sai ta ba ka mamaki a harkar kwallo don sau da yawa an sha ganin irin haka a tarihin kwallo”, inji Emenike a lokacin da yake hira da manema labarai jim kadan da tashi wasansu da Malawi a Kalaba.
Ya kara da cewa ganin cewa Najeriya ce zakara a Nahiyar Afirka a wannan lokaci, kowace kasa za ta dage ne wajen ganin ta samu nasara akan ta, don haka akwai bukatar su yi taka-tsan-tsan wajen cigaba da kare martabar Najeriya.
Super Eagles ta shirya tunkarar kowace kasa a gasar neman zuwa cin kofin duniya -Emmanuel Emenike
Dan kwallon gaba a kungiyar Super Eagles Eammnuel Emenike ya bayar da tabbacin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles za ta haye gasar cin kofin…