Kungiyar Kwallon kafa ta Super Eagles, ta kammala gasar cancantar shiga gasar AFCON ta 2021 ba tare sa an yi nasara a kanta ba.
Kungiyar wacce ta lashe gasar kofin Afrika har uku, ta lallasa Lesotho da ci uku da nema a filin wasa na Teslim Balogun da ke jihar Legas.
- Gidauniyar Daily Trust ta gudanar da taron karawa ’Yan Jaridu sani
- Aguero zai yi bankwana da Manchester City a karshen kaka
- Batanci ga Annabi: An kashe matashi an kona gawarsa a Bauchi
- Ganduje ya fitar da N8.9bn na gina Gadar Sama a Hotoro
Victor Osimhen, dan wasan gaba na kungiyar Napoli ne ya fara zura kwallo a minti na 22 inda a daidai wannan lokaci wani dan kallo ya afka cikin filin wasa don taya ‘yan wasan murna.
Sai dai ba jimawa jami’an tsaro suka cafke shi tare da ficewa da shi daga filin wasan.
A minti na 50 ne dan wasa Oghenekaro Etebo, ya sake zura kwallo ta biyu, wanda hakan ya kara wa ‘yan kallo armashi.
Sai kuma a minti na 83, Paul Onachu, ya zura kwallo ta karshe.
Najeriya ta kare rukuni na L da maki 14, daga wasanni shida da suka buga, inda suka yi nasara a wasanni hudu da kuma canjaras a biyu.