A ranar Talata, 17 ga watan Nuwamban bana ne kungiyar wasan kwallon kafa ta Najeriya, Super Eagles ta buga wasanta na karshe na bana, inda aka tashi kunnen doki a wasan.
An buga wasan ne wanda na neman gurbin shiga Gasar Kofin Nahiyar Afirka ne a filin wasa Freetown da ke kasar Saliyo.
Kafin wannan wasan, Saliyo ta rike Najeriya da ci hudu da hudu a filin wasa na Samuel Ogbemudia da ke birnin Benin na Jihar Edo, duk da cewa Najeriya ta fara ne da ci hudu da daya, kafin Saliyo ta farke.
Kafin wadannan wasannin a gida da waje, Najeriya ta buga wasanni biyu ne kawai.
A ranar 9 ga Oktoban bana, kasar Algeriya ta doke Najeriya da ci daya da name a wasan sada zumunta.
Haka kuma a ranar 13 ga Oktoban, an tashi kunnen doki tsakanin Najeriya da Tunisia a wani wasan na sada zumunta.
Ke nan a bana, jimilla Najeriya ta doka wasa hudu, ta yi kunnen doki uku, an ci ta daya.