Gwamnatin Jihar Kano ta rufe wasu kwalejoji koyar da harkokin kiwon lafiya 26 da ke aiki ba bisa ka’ida ba a sassa daban-daban na jihar.
A cewar gwamnatin, yaduwar ire-iren makarantun a baya-bayan nan, yana da illa ga lafiyar jama’a, ci gaban ilimi da ingantaccen tsarin kiwon lafiya baki daya.
- Yadda rashin tsaro ke barazana ga Zaben 2023 a Arewa
- Kotu ta sa ranar sauraron martanin da ake yi wa tuhumar Abduljabbar
Cikin sanarwar da Ma’aikatar Lafiya ta jihar ta aike wa manema labarai ranar Juma’a mai dauke da sa hannun jami’ar hulda da jama’a ta ma’aikatar, Hajiya Hadiza Namadi, ta ce makarantun za su ci gaba da kasancewa a rufe sai bayan kammala gudanar da bincike a kansu.
Sanarwar ta kara da cewa wasu daga cikin makarantun ba su da mazauni na dindindin, sannan kuma suna koyar da wasu kwasa-kwasai da suka saɓa da tsarin manhajar koyar da kiwon lafiya, tare kuma da tatsar dalibai da iyayensu maƙudan kuɗaɗe na babu gaira-babu-dalili.
A karshe, sanarwa ta shawarci mazauna jihar da su guje wa irin waɗannan makarantu, ta hanyar zuwa makantun da gwamnati ta bai wa lasisi.
Ga makarantun da abin ya shafa:
Kwalejin Kiwon Lafiya ta Unity da ke Dorayi Karama a Karamar Hukumar Gwale da kuma cibiyarta a Karamar Hukumar Dambatta.
Kwalejin Kiwon Lafiya ta Khalil da ke Titin Zariya daura da Gadar Lado a Karamar Hukumar Gwale da kuma cibiyoyinta a Kananan Hukumomin Dambatta da Wudil.
Kwalejin Kiwon Lafiya ta Shima da ke Karamar Hukumar Gezawa.
Kwalejin Kiwon Lafiya ta Autan Bawo da ke Karamar Hukumar Rano.
Kwalejin Kiwon Lafiya ta Trustee da ke Unguwar Jakara a Karamar Hukumar Dala, da kuma cibiyarta a Unguwar Bachirawa da ke Karamar Hukumar Ungogo.
Kwalejin Kiwon Lafiya ta Eagle da ke Karamar Hukumar Bichi.
Kwalejin Kiwon Lafiya ta Albakari da ke Unguwar Rijiyar Zaki a Karamar Hukumar Ungogo.
Kwalejin Kiwon Lafiya ta Jamatu da ke Karamar Hukumar Kura.
Kwalejin Kiwon Lafiya ta Savanna da ke Karamar Hukumar Wudil.
Kwalejin Kiwon Lafiya ta Ahmadiyya da ke daura da Ofishin Hukumar Zabe (INEC).
Kwalejin Kiwon Lafiya ta Jamilu Chiroma da ke titin Zungeru a Unguwar Saboon Gari.
Kwalejin Kiwon Lafiya ta Sir Sanusi da ke Unguwar Matan Fada a Karamar Hukumar Nasarrawa.
Kwalejin Kiwon Lafiya ta Aminu Ado Bayero da ke Unguwar Dandishe a Karamar Hukumar Dala.
Kwalejin Kiwon Lafiya ta Awwab da ke Unguwar Salanta a Karamar Hukumar Gwale.
Kwalejin Kiwon Lafiya ta Gwarzo Unity da ke Karamar Hukumar Gwarzo.
Kwalejin Kiwon Lafiya ta Al-wasa’u da ke Unguwar Tudun Fulani a Karamar Hukumar Nassarawa.
Kwalejin Kiwon Lafiya ta Kanima Academy da ke Unguwar Zangon Dakata a Karamar Hukumar Nassarawa.
Kwalejin Kiwon Lafiya ta Muslim da ke titin Zungeru a Karamar Hukumar Fagge.
Kwalejin Kiwon Lafiya ta Utopia da ke Unguwar ’Yankaba a Karamar Hukumar Nassarawa.
Kwalejin Kiwon Lafiya ta Jama’a da ke Unguwar Na’ibawa ’yan-lemo a Karamar Hukumar Tarauni.
Kwalejin Kiwon Lafiya ta Kauthar da ke titin Jos a Karamar Hukumar Tudun Wada.
Kwalejin Kiwon Lafiya ta Shanono a Karamar Hukumar Shanono.
Kwalejin Kiwon Lafiya ta Jakara Garden da ke titin filin jirgin sama a Karamar Hukumar Nassarawa.
Kwalejin Kiwon Lafiya ta mata zalla ta Habib Faruq da ke Gidan Kara a Unguwar Kurna.
Kwalejin Kiwon Lafiya da ke Firamaren Bachirawa a Karamar Hukumar Ungogo.
Kwalejin Kiwon Lafiya ta Faudiyya da ke Danrimi a Unguwar Rijiyar Lemo ta Karamar Hukumar Fagge.