✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sun yanka matar makwabcinsu bayan sun yi mata fyade

A cikin watan azumi suka yi wa matar fyade suka kuma yanka ta

‘Yan sanda ta kama wasu matasa biyu da suka yi wa matar makwabcinsu fyade suka kuma kashe ta a garin Kakumi da ke Karamar Hukumar Baure ta jihar Katsina.

Mai magana da yawun Rundunar ‘Yan Sanda jihar, Gambo Isa, a ranar Juma’a ya ya matasan sun yi aika-aikan ne cikin azumi da misalin karfe 1 na daren 11 ga watan Mayu, 2020.

Gambo Isa ya ce matasan sun ketara gidan makwabcinsu, suka yi wa matarsa fyade, amma da suka lura ta gane dayansu, sai suka yi mata yankan rago don asirinsu ya rufu.

Yan sanda sun gano wayar hannun matar a wajen daya daga cikin matasan, aka kuma gano rigar da dayan ke sanye da ita a lokacin da suka kashe matar.

Wata majiya ta ce daya daga cikin wadanda ake zargin ya rude matuka a lokacin da aka je makabarta binne matar.