✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sun yi wa maigadi yankan rago don su gaji gidan da ba nasu ba

Wadansu da ake zargin suna son su gaji wani gida da ba nasu ba, sun kashe mai gadin gidan ta hanyar yi masa yankan rago,…

Wadansu da ake zargin suna son su gaji wani gida da ba nasu ba, sun kashe mai gadin gidan ta hanyar yi masa yankan rago, a Unguwar Garuje da ke bayan Kasuwar danmagaji a gundumar Tukur-Tukur karamar Hukumar Zariya, Jihar Kaduna.
Mutanen unguwar sun ce an kashe makwabcin nasu da suka shafe shekara 45 tare mai suna Sunday mai kimanin shekara 65 wanda bayan gadi yana sayar da masara a Kasuwar danmagaji a tsawon lokaci.
Wani da Aminiya ta tuntuba a unguwar da bai so a ambaci sunansa ba wanda kuma da shi aka yi zirga- zirga kan wanda aka hallakan, ya ce da misalin karfe 11:30 a dare a ranar Alhamis, Mai unguwar Garuje ya buga masa kofa ya ce masa ga abin da ya faru don haka ya fito domin su isa wurin, “Sai muka hadu mu biyar makwabtan wanda aka kashen, wadanda su ne suka zo da bayanin, ni kuma na ba Mai unguwa shawara cewa mu wuce wurin ’yan sanda mu sanar da su tukunna, da muka sanar da su cikin daren muka zo muka shiga gidan muka gan shi kwance cikin jini an yanka wuyansa kuma an farke cikinsa, sai ’yan sanda suka nemi bayani daga makwabtansa  inda cikin daren aka je gidan wanda ake zargi a Wusasa mai suna Bomboy aka yi sa’a kayan da ke jikinsa duk jini kuma ya yi rauni a hannunsa. Bayan an zo da shi ofishin ’yan sanda na danmagaji sai ya ambaci wani abokinsa mai suna Uche, aka je aka kamo shi, an tarar da shi yayi rauni a kansa kuma yana kokarin wanke jini a jikinsa. Da alama sun yi gumurzu da marigayi Sunday kafin su kashe shi. Daga nan aka kamo mahaifiyar Bomboy mai suna Philo wadda aka fi sani da Maman Bomboy aka dauki gawar aka tafi da ita Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika,” inji shi.
Mai unguwar Garuje, Malam Muhammadu Bello ya ce, a ranar Alhamis din wadansu mutanen unguwarsa sun kai masa rahoton cewa an kashe makwabcinsu Sunday mai gadin gidan Bature, kuma bayan sun sanar da ’yan sanda sai suka je gidan suka tarar da Sunday kwance cikin jini. ’Yan sanda suka dauki gawar, kuma cikin daren suka yi wa wani abokin zamansa a daki daya a gidan Baturen, mai suna Bala Amfani tambayoyi da kuma Sule Gashin Baki wanda makwabcinsu ne da ya kai gudunmawa. Ya ce wannan ya jawo aka kamo Bomboy da mahaifiyarsa Philo da kuma abokin zarginsa da kisan mai suna Uche dan kabilar Ibo da yake sana’ar yankan gasket a Kasuwar danmagaji.
Mai unguwar ya shaida wa Aminiya cewa ainihin mai gidan da marigayin yake ciki Bature ne wanda shi ne ya fara gina gida a unguwar sama da shekara 50, yana cikin Mishan na Wusasa kuma ya rasu shekara 30 da suka wuce. Ya ce “Yana da mace bakar fata wanda ta rasu, ita kuma asalinta ’yar Wusasa ce sai dai dukkansu ban san sunansu ba, tun ina yaro na sansu a nan wurin kuma a sanina ba su haihu ba sai dai suna da wata ’yar riko. Sunday ne yake tare da Baturen tsawon lokaci yana yi masa gadin gidan kuma yana kasuwanci a danmagaji, kuma ana zaune lafiya da shi bai taba fada da kowa ba, don haka kowa ke kaunarsa, kwatsam muka wayi gari an kashe shi, yanzu kuma maganar na hannun ’yan sanda suna gudanar da bincike, kuma na sanar da Dagacina,” inji shi.
A binciken da Aminiya ta yi a unguwar an shaida mata cewa kamar kwana hudu kafin aukuwar lamarin Sunday ya yi kukan ana barazana ga rayuwarsa a kan wannan gida duk da maganar gidan tana kotu ana takaddama a kan wadanda za su gaje shi, saboda Baturen ba ya da ’yan uwa kuma matar da ya aura ba su taba haihuwa ba. Don haka wadanda suke son su gaji gidan ne suke yawan yi masa barazanar kashe shi.
Mataimakin Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kaduna mai kula da Shiyya ta daya, Abdullahi Ibrahim wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce wadanda ake zargi da kisan sun tabbatar da cewa su suka yi,  kuma su biyu ne an kama su kuma da wukaken da suka yi kisan. Ya ce asalin gidan na wani Bature ne ya ce wanda ake zargin ya ce dalilin da ya sa suka kashe marigayin shi ne wai yana bin sa kudi kuma ya ki biyansa, na biyu kuma da ma suna so ne yadda za a yi ya fita daga gidan, to tunda ya amsa laifinsa ya tabbatar to za su tura su Babban Kotu.