✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sun kashe dan makwabci bayan karbar kudin fansa

Mutanen da suka sace dan makwabcinsu, suka kashe shi bayan karbar kudin fansa sun shiga hannu.

An kama wani wanda ya sace dan makwabcinsa, ya kashe shi bayan karbar kudin fansa daga iyayen yaron a Jihar Kaduna.

Mutumin mazaunin unguwar Badarawa a garin Kaduna, ya hada baki ne da wani makwabcinsu, wanda tsohon soja ne suka sace ’yaron, mai suna Muhammad Kabir, dan aji biyu a makarantar firamare.

Kakakin ’yan sandan Jihar Kaduna, Muhammad Jalige ya tabbatar wa Aminiya cewa mutanen biyu na tsare a hannunsu, kuma sun amsa laifin da ake zargin su da aikatawa.

“Daya daga cikinsu makwabcinmu ne, dayan kuma tsohon soja ne, mazaunin unguwarmu.

“Sun fara kai shi Zariya daga nan suka wuce da shi Kano inda aka tsinci gawarsa a kwalbati, bayan an biya su kudin fansa Naira miliyan biyar,” inji wan mamacin, Abdulrahman.

Lokacin da ake gudanar da Sallar Jana’izar Muhammad a masallacin Sultan Bello, Kaduna.

Tuni dai aka yi wa Muhammad jana’iza a Masallacin Sultan Bello da ke garin Kaduna a ranar Asabar.

An yi kwanaki ana neman Muhammad wanda daga fitarsa kofar gida ba a sake ganinsa ba, kafin masu garkuwar suka kira iyayensa suna neman kudin fansa.

Wata majiya ta ce makwabcin da ya kitsa sace yaron na daga cikin masu yi wa iyayen jaje, tare da addu’ar Allah Ya tona asirin wadanda suka sace shi.

Marigayi Muhammad Kabir.

Majiyar ta ce da farko masu garkuwar sun nemi a ba su kudin fansa Naira miliyan 50, kafin su rage zuwa miliyan 35, daga karshe dai aka daidaita da su a kan Naira miliyan biyar.

Sai dai kuma bayan biyan kudin fansar ba su dawo da yaron ba, ana cikin haka ne, aka samu labarin ganin makwabcin tare da shi a wata tashar mota a Kano.

Muhammad tare da ‘yan ajinsu a lokacin ziyarar da suka kai Filin Jirgin Sama na Kaduna. Shi ne uku a tsaye (da hannunsa a kumatunsa).

Bidiyon daya daga cikin wadanda ake zargin ya nuna shi yana cewa sun makure shi ya mutu ne saboda ya gane su.

Wasu hotunan da aka gano sun nuna irin azabtarwar da masu garkuwar da suka yi wa yaron da aka gano gawarsa a cikin wani kwalbati.

Majiyarmu ta ce wanda ake zargin ya ce karo na shida ke nan suna garkuwa da mutane.