✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sukurkucewar al’amuran al’umma: Sabubba da maganinsu (2)

Daga Sheikh Ali Abdur-Rahman Al-Huzaifi, Masallacin Annabi (SAW), MadinaYa ’yan uwa Musulmi!  Duk lokacin da bala’i ya samu al’umma, abu na farko da ya wajaba…

Daga Sheikh Ali Abdur-Rahman Al-Huzaifi, Masallacin Annabi (SAW), Madina
Ya ’yan uwa Musulmi!  Duk lokacin da bala’i ya samu al’umma, abu na farko da ya wajaba su yi, su hanzarta tuba, tuba ta gaskiya. Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma ku tuba zuwa ga Allah gaba daya, ya ku muminai! Tsammaninku, ku samu babban rabo.” (k:24:31).
Akwai bukatar kowane Musulmi ya rika tuba ta gaskiya. Ba mamaki wani ya ce: “Mene ne dangantakar tuba ta da kyautatuwar al’amuran sauran al’ummar Musulmi?”
To abin da ya kamata a gaya masa shi ne, yi wa Allah da’a da biyayya shi ke kawo duk wani alheri a nan duniya da Lahira, kuma abin da ke jawo aukuwar munanan abubuwa shi ne saba wa Allah.  Kuma a gaya masa cewa tubar da kowane mutum zai yi za ta kawo alheri da yawa kuma ta hana aukuwar bala’i a kan al’ummar Musulmi.
Kuma wajibi ne Musulmi su hada kai su fuskanci wannan duniya da ke canjawa, kuma take neman a canja akidar Musulunci a kawar da kyawawan dabi’unsa da dokokinsa.
An halaka al’ummomin da suka gabata ne saboda samuwar masu aikata zunubi da yawa da karancin mutanen kirki cikinsu. Kuma laifin mutum daya yana iya jawo halakar al’ummar gari ko kasa. Domin Allah Ya halaka Samudawa ne saboda daya daga cikinsu ya kashe taguwa. Kuma Ya saukar da annoba ga Bani Isra’ila – duk da cewa Annabi Musa da Annabi Haruna (AS) suna cikinsu – saboda wadansunsu sun yi zina. Allah Madaukaki Ya ce game da wasu al’umma da Ya halaka su: “Saboda haka kowanensu Mun kama shi da laifinsa: wato daga cikinsu akwai wanda Muka aika iskar tsakuwa a kansa; kuma daga cikinsu akwai wanda tsawa ta kama; kuma daga cikinsu akwai wanda Muka birkice kasa da shi; kuma daga cikinsu akwai wanda Muka nutsar (a ruwa). Ba ya yiwuwa ga Allah Ya zalunce su, amma sun kasance kansu suke zalunta.” (k:29:40).
Zainab Bint Jahsh (RA) ta ce: Manzon Allah (SAW) ya ce: “Bone ya tabbata ga Larabawa, saboda wani bala’in da zai auka musu. Yau katangar Yajuju wa Majuju ta bude zuwa kwatancin haka”. Sai ya yi nunin kwatancin ta yin kuri da manuniyarsa da babban yatsa. Sai Zainab (RA) ta ce: “Sai na ce, ‘ya Manzon Allah! Shin za a halaka mu ne alhali akwai mutanen kirki a cikinmu?’ Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Eh, a lokacin da zina da giya suka yadu.”
Don haka kada ku yi sakaci da batun tuba ko kadan, domin ita ce kadai hanyar fita daga tsanani. Ku yi riko da Littafin Allah da Sunnar ManzonSa (SAW), domin su ne hasken shiriya da suke raba mutane da duhu da tabewa.
’Yan uwa a cikin imani! Addinin Musulunci ya umarci Musulmi da hadin kai kuma ya hane su daga rarrabuwa. Allah Madaukaki Ya ce: “Ku yi riko da igiyar Allah gaba daya, kada ku rarraba.” (k:3:103). Kuma Ya ce: “Kuma kada ku yi jayayya har ku raunana, kuma iskarku (karfinku) ta tafi, kuma ku yi hakuri.” (k:8:46).
Yayin da addinin Musulunci ya umarci Musulmi da hadin kai a tsakaninsu, hakan ba yana nufin a rika kai hari ga wadanda ba Musulmi ba ne ko a tauye musu hakkokinsu da shari’ar Musulunci ta ba su.
Da wadanda ba Musulmi sun fahimci adalcin Musulunci da kyawawan halayensa da sun rugume shi, kuma ba za su zargi Musulunci, saboda kurakuran da wadansu Musulmi suke yi ba. Allah Madaukaki Ya ce: “Ka ce (ga mutane): “Ku zo, in karanta abin da Ubangiji Ya haramta muku…” Wajibi ne a kanku kada ku yi shirkin (hadin) komai da Shi, kuma ga mahaifa biyu (ku kyautata musu) kyautatawa, kuma kada ku kashe ’ya’yanku saboda (gudun) talauci, Mu ne Muke azurta ku da su, kuma kada ku kusanci abubuwan alfasha, abin da ya bayyana daga gare ta da abin da ya boyu, kada ku kashe rai wanda Allah Ya haramta (girmama) face da hakki. Wannan ne (Allah) Ya yi muku wasiyya da shi: tsammaninku, kuna hankalta.” (k:6:151).
’Yan uwa a cikin imani! Ku ji tsoron Allah matukar jin tsoronSa, ku nemi kusanci zuwa gare shi ta hanyar aikata kyawawan ayyuka da kaurace wa zunubai. Ku aika kyawawan ayyuka kafin ku sadu da Shi, kuma ku ribaci rayuwarku ta duniya. Allah Madaukaki Ya ce: “Ya ku wadanda suka yi imani! Ku bi Allah da takawa, kuma rai ya dubi abin da ya gabatar domin gobe, kuma ku bi Allah da takawa. Lallai Allah Mai kididdigewa ne ga abin da kuke aikatawa.” (k:59:18).
Ku tanadi amsoshin da za su kubutar da ku daga wahalhalun ranar kiyama. Manzon Allah (SAW) ya ce: “ Duga-dugan dan Adam ba za su gushe ba a ranar kiyama, har sai an tamabye shi kan rayuwarsa yaya ya tafiyara da ita da kuruciyarsa yaya ya yi amfani da ita da dukiyarsa yaya ya same ta kuma yaya ya kashe ta da kuma iliminsa yaya ya yi da shi.”