✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sudan: Sojoji sun dawo da fira Minista Hamdok kan mulki

Mako hudu bayan sun yi masa juyin mulki suka dawo da shi kan kujerarsa tare da alkawarin sako fursunonin siyasa da ke hannunsu

Sojojin kasar Sudan sun dawo da Fira Minista Abdulla Hamdok kan mulki, kasa da wata guda bayan sun yi masa juyin mulki.

A ranar Lahadi aka rattaba hannu da shugaban sojojin da suka yi juyin mulkin, Janar Abdel Fattah al Burhan, kan yarjejeniyar dawo da mulkin dimokuradiyya a kasar, bayan sako Fira Minista Hamdok, wanda aka kifar da gwamnatinsa ranar 25 ga watan Oktoba, 2021.

An kulla yarjejeniyar ce bayan masu shiga tsakani sun sasanta bangarorin da suka hada da sojojin da bangarorin siyasa masu hamayya da juna da kuma tsoffaffin ’yan tawayen kasar.

A karkashin yarjejeniyar mai sharudda 11, Fira Minista Hamdok zai jagoranci gwamnatin rikon kwarya.

Zai kafa majalisar ministoci da za ta kunshi kwararru da sojoji da sauran wadanda suka dace domin tabbatar da daidaito a kasar.

Sojojin kuma za su sako duk fursunonin siyasa da ke tsare a hannunsu tun lokacin da aka yi juyin mulkin.

Kundin tsarin mulkin kasar da aka samar a 2019 bayan hambarar da gwamnatin Shugaban Umar Al Bashir za ta ci gaba da da aiki.

Tun bayan juyin mulkin na ranar 25 ga watan Oktoba, 2021, masu ruwa da tsaki a Sudan, karkashin inuwar kungiyar ‘Sudan Initiative’, suka yi ta kai-komo domin dawo da mulkin dimokuradiyya a kasar.

Juyin mulkin ya haifar da zanga-zangar da ta ki ci ta ki cinyewa na adawa da sojojin inda aka yi ta kone-kone da tare hanyoyi.

A wasu lokuta sojoji sun bude wuta a kan masu zanga-zangar, suka kashe wasu tare je jikkata wasu.

– An samu rabuwar kai

Yarjejeniyar ta haifar da rabuwar kai tsakanin al’ummar Sudan, inda wasu daga cikin masu zanga-zangar suka yi watsi da ita.

Bangarorin da suka hada da kungiyoyin kwararru da magoya bayansu (Milyoniya) sun nesanta kansu da sulhun, tare da zargin Fira Minista Hamdok da cin amanarsu.

Masu zanga-zangar sun ce babu ruwansu da abin Hamdok ya yi, suna neman a hukunta wadanda suke da hannu a kashe masu zanga-zanga ko gwamnatin da sojoji ke da ta cewa a ciki.

%d bloggers like this: