Sojojin kasar Sudan sun rushe gwamnatin rikon kwaryar kasar tare da ayyana dokar ta-baci.
Sojojin sun kuma tsare shugabannin kasar, a daidai lokacin da ake ci gaba da zanga-zanga a Khartoum, babban birnin kasar.
- “Juyin mulki”: An tsare shugabannin farar hula na gwamnatin Sudan
- An yi garkuwa da masu ibada suna tsaka da bauta a coci
Dubun-dubatar jama’a ne dai suka shiga zanga-zangar, duk kuwa da rahotannin bude musu wutar da aka bayar.
Tun bayan hambarar da gwamnatin Shugaba Omar Al-Bashir shekaru biyu da suka gabata da kuma kafa gwamnatin rikon kwarya a kasar, an sami baraka tsakanin sojoji da fararen hula a kasar.
Janar Abdel Fattah Burhan, wanda shi ne sojan da ya jagoranci gwamnatin rikon kwaryar wacce ta kunshi fararen hula dai ya zargi ’yan siyasar kasar da iza wutar rikicin.
An bayar da rahoton cewa wasu mutane dauke da makamai sun yi awon gaba da jami’an gwamnatin rikon kwarya ta Sudan da dama.
An ce wasu sojoji da ba a san ko su wane ne ba sun tsare ministoci akalla hudu jim kadan da ketowar alfijir ranar Litinin.
Har yanzu dai babu tabbas a kan ko wane ne ke da alhakin kama jami’an – rundunar sojin kasar ta ki ta ce uffan a kan lamarin.
Wasu rahotanni sun nuna cewa an kama Firai Minista Abdallah Hamdok, wanda farar hula ne, ko da yake ba a tabbatar da hakan ba.
BBC ta bayar da rahoton cewa babu intanet a Khartoum, babban birnin kasar, yayin da wasu hotuna da ke nuna gungun fusatattun mutane suna kona tayoyi a kan tituna suka fara karakaina a kafafen sadarwa na zamani.
AFP ya ruwaito cewa a birni na biyu mafi girma a kasar ma, wato Omdurman, an katse hanyoyin sadarwa na intanet, yayin da gidajen rediyo da talabijin ke saka wakokin kishin kasa.
Rahotanni sun ce yanzu haka n rufe filin sauka tashin jiragen birnin Khartoum, yayin da aka soke dukkan jiragen da ke zuwa kasashen waje.
Juyin mulkin dai na zuwa kusan wata daya bayan an hambarar da gwamnatin Alpha Conde na kasar Guinea.