Wani Likitan Fida da ya kware kan dashen fatar mutum a kasar Indiya mai suna Dokta Subodh Kumar Singh da ake yi wa lakabi da Jarumin Likita, yana samun yabo bayan ya yi tiyata ga sama da mutum dubu 37 kyauta don gyara tsagewar furucin yara da tsagewar lebensu ko mokadewar lebba.
A cewar Cibiyar Yaki da Yaduwar Cututtuka (CDC), tsagewar leve da mokadewar bangarorin fatar baki, suna yin faruwa ne tun a lokacin haihuwa
lokacin da lebe ko bakin jariri ba su yi daidai ba yayin daukar juna biyu.
- An kashe mutum 5, an kone gidaje a rikicin manoma da makiyaya a Ogun
- Majalisar Dinkin Duniya ta roki Amurka ta rufe kurkukun Guantanamo
Wannan na haifar da matsaloli iri-iri da suka hada da rashin samun madara a
matsayin jarirai, kuma hakan na haddasa wa masu larurar haduwa da cin zarafi da nuna masu wariya.
Ana iya gyara nakasar da bayan haihuwa ta yin tiyatar gyaran fata (plastic surgery), amma hakan, ba su samuwa ga iyalai matalauta da suka fi bukatarsu.
A Indiya dai an samu wannan likita a matsayin mai tallafa wa dubbban jarirai da yara, yana gyara tsagewar lebbansu
ko bangarorin fatar bakinsu a kyauta, don haka ya ba su dama don samun ingantacciyar rayuwa.
An haifi wannan jarumin likita ne a cikin iyali masu tawali’u a garin Varanasi a
Jihar Uttar Pradesh ta Indiya, Dokta Singh ya samar wa kansa nasara a lokacin kuruciya, inda ya sadaukar da aikinsa don taimaka wa mabukata,
maimakon neman kudi.
Bayanai sun ce bayan likitan ya rasa mahaifinsa, wani ma’aikacin jirgin kasa, lokacin da yake dan shekara 13, Singh da ’yan uwansa uku sun yi ta neman abin da za su ciyar da iyalansu ta hanyar sayar da kyandir da aka yi a gida da sabulu da tabarau a kan tituna da cikin shagunan unguwanninsu.
’Yan uwan Dokta Subodh sun daina karatu don su tallafa wa iyalansu, amma sun tabbatar da cewa Subodh ya ci gaba da karatunsa kuma ya cika burinsa na zama likita.
Kuma duk da cewa, yana taimakon ’ya’yan ’yan uwansa gwargwadon iyawarsa, ya yi ayyuka da dama a lokacin da yake neman ilimin.
Subodh ya kammala karatunsa a Cibiyar Kimiyyar Kiwon Lafiyar Jama’a, a fannin aikin tiyata na gaba daya, kuma ya kware a aikin tiyatar sauya fata.
“’Yata ta ba ni karfin juriya da habaka fahimtata ga mutanen da ke fama da gwagwarmayar yau da kullun,” Dokta Singh ya bayyana wa kafar labarai The
Better India.
“Wahalhalun da suke fuskanta sun sa na fahimci halin juncin rayuwa da suke
fuskanta kuma na danganta su da su. Zama likita ya sa ni cikin matsayi na taimaka wa mutane da yawa. Ina so in kyautata rayuwar marasa galihu,” inji shi.
Fahimtar cewa jarirai da yaran da aka haifa da tsagewar lebe ko mokadewa suna bukatar taimako, sai likitan ya fara shirya cibiyoyin jinya kyauta tare da taimakon masu fama da cutar gwargwadon iyawarsa.
Ba da dadewa ba aka fahimci kokarinsa ta hanyar Kungiyar Smile Train, wata kungiya ta duniya da ta mai da a hankali kan yi wa yara tiyatar lebe ko tsagewar fatar baki.
Tare da goyon bayansu da na sauran
kungiyoyi masu zaman kansu, Dokta Singh ya iya taimaka wa dimbin mutanen da ya yi wa tiyata kyauta.
“Wadannan jariran ba za su iya samun madara kamar yadda suke bukata ba. Mutane da yawa suna mutuwa saboda
rashin abinci mai gina jiki kuma sau da yawa ci gabansu ya takure. Yaran da wuya su yi amfani da harcensu wajen
yin magana, hakan na haifar da matsalar magana,” inji Dokta Subodh Kumar Singh.
Ya ce, irin wannan larurar yake gyarawa. “Yaran sukan daina zuwa makaranta saboda maganganun wadansu ko cin
zarafinsu saboda yanayinsu.
“Suna fuskantar kalubale wajen neman aikin yi ko samun karvuwa. A lokuta da dama, ana zargin uwa da haifar jariri da irin wannan larura saboda ta haifi yaro da rababben lebe. Hakan yana taba tunanin iyaye. Amma yin tiyata zai iya magance shi duka,” inji shi.
Tun lokacin da ya fara aiki da karamin albashi a shekarar 2004, Dokta Singh ya yi wa yara da manya sama da dubu 37,
tiyata kyauta tare da taimakon Kungiyar Smile Train, ya kuma samu damar horar da wadansu likitoci da dama a fadin
Indiya don gyara masu fama da matsalolin da suka shafi haihuwa da fatar wata rana za su iya kafa wata cibiya ta kasa don gyara tsagewar lebe ta hanyar tiyata.
Dokta Subodh ya kara da cewa, “Ina alfahari da samun ikon canja rayuwar mutane da yawa. Tiyata daya tana tasiri ga dangi fiye da iyali da rayuwar kowane mutum. Ba abin da ya fi ba ni farin ciki kamar in hada dangin da suka karbi surukarsu bayan an yi musu tiyata kuma ba sa zarginta da nakasa nan gaba.”