✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Steven Gerrrard ya zama kocin Aston Villa

Ya maye gurbin Dean Smith a matsayin kocin Aston Villa.

Tsohon dan wasan Liverpool da Ingila, Steven Gerrrard ya zama sabon kocin kungiyar Aston Vila, inda zai maye gurbin Dean Smith.

Gerrard ya baro kungiyar Rangers ta Scotland ce bayan ta jagoranci kungiyar ta lashe Firimiyar Scotland na farko a shekara 10.

A kakar bara, kungiyar ta Rangers ta ba rasa wasa ko daya ba.

A wasannin da ya jagoranci kungiyar, ya lashe kashi 56.5 cikin 100, sannan ya lashe kofi daya.

A ranar 11 ga Disamba ce Gerrard zai jagoranci kungiyar Aston Villa zuwa filin Anfield domin fafatawa da Liverpool a Gasar Firimiyar Ingila.