✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sterling Bank ya cancanci yabo saboda bullo da PaywithSpecta

Tsarin PaywithSpecta da Sterling Bank ya bullo da shi ya taimaka wajen bunkasa kasuwanci.

Shugaban kamfanin Al-Ummur Ventures Limited masu sayar da yadduka a sananniyar kasuwar nan ta Kasuwar Barci da ke Tudun Wada Kaduna, shi ne Alhaji Umar Nasiru. 

A tattaunawarmu da shi ya yaba wa bankin Sterling Bank Plc saboda bullo da tsarin PaywithSpecta, yana mai cewa tsarin ya taimaka wajen bunkasa harkar tasa.

A matsayinka na dan kasuwa, wace hanya ko dabara kake bi a yanayin da harkar kasuwanci ke ciki a 2021?

Daga cikin manyan matsalolin kasuwanci a yanzu akwai batun kudi, yawancin mutane ba su da jari sosai.

Abin da Sterling Bank ke yi na taimakon kasuwancin abokan huldarsa na taimakawa matuka a wannan yanayi saboda ba a cika samun rancen gwamnati ba.

Tsarin bankin na ba da rance ya cancanci yabo.

 

Ta wace hanya tsarin Sterling Bank na ba da rance ga kananan kamfanoni ya taimaka wa kasuwancinka? 

PaywithSpecta ya kawo kyakkyawan sauyi matuka. Bayan Sterling Bank ya gabatar min da shi sai da na dan yi fama wajen wayar da kan kwastomomina cewa su rika amfani da tsarin.

Ba abu ne mai sauki ba  ka iya gamsar da mutane a yankin Arewa cewa su karbi rancen banki. 

Amma Ni na yi sa’a sosai saboda kwastomomina sun gamsu suka kuma karbi tsarin; yanzu haka suna farin ciki da ni.

Kuma ni kaina yana taimaka wa kasuwancina. Saboda haka tsarin PaywithSpecta na taimaka wa kasuwancina. 

 

A ina ka fara samun bayani kan PaywithSpecta? 

Jami’in da ke kula da asusun bankina ne ya fara gabatar min da bayani kan PaywithSpecta. 

A lokacin ban dauki abin da muhimmanci ba, amma daga baya sai na samu wani manajan Sterling Bank ya yi min cikakken bayani.

Abin da na lura tun da na fara amfani da shi shi ne ribar da suke karba ba yawa. Idan suka ci gaba a haka, to sauran bankuna za su zama ba su da zabi face su ma su bi sahu.

 

Wadanne tsare-tsaren PaywithSpecta kake tallata wa abokan huldarka? 

Harkar yaduka muke yi, saboda haka duk lokacin da suka zo sayen kayamnu masu sauki sai mu yi amfani da damar mu yi musu magana kan amfani da PaywithSpecta. 

 

Ta wace hanya tsarin ke yin tasiri a kasuwancinka? 

Ai tuni na fara ganin faidarsa saboda mutumin da a baya yake sayen kayan Naira miliyan biyu yanzu yakan sayi na miliyan N2.5 ba tare da ya ci bashi mai yawa ba. Tabbas abu ne mai kyau.

 

Shin za ka ba sauran ’yan kasuwa shawarar amfani da shi?

Ina shawaratar ’yan kasuwa su rungumi PaywithSpecta saboda saukinsa. Zan kuma yi musu bayani cewa taimakon su bankin ke yi wajen bunkasa kasuwancinsu ta tsarin na PaywithSpecta.

 

Ta yaya kake wayar da kan kwastomominka game da PaywithSpecta?

Ina kara wayar da kai a kansa saboda ina da kwastomomin da suka fara cin gajiyarsa daga bayanan da na yi musu a baya har suka shiga PaywithSpecta. 

Ina kuma ci gaba da yi wa kwastomomi bayanin alfanon tsarin idan suka zo yin sayayya a wurina. 

 

Wace irin karin babbar dama kake son samu a 2021?

Dama masu yawa. Ina fata bankin zai bullo da karin hanyoyi da taimaka harkokin kasuwanci su bunkasa, musamman yanzu da ’yan kasuwa ba su cika samun tallafin gwamnati ba.

Idan ba da irin wadannan abubuwan ba, kasuwanci  tsayawa cik zai yi, ga shi kuma tasirin karuwar yawan al’umma kan tattalin arziki sai karuwa yake ta yi.