‘Yar Majalisar Tarayya daga Jihar Anambra, kuma tsohuwar Minista a Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama, Sanata Stella Oduah ta sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.
Sanata Oduah ta sanar da ficewarta daga jam’iyyar PDP a ranar Alhamis, a Abuja inda Shugaban Rikon na jamiyyar APC kuma Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya jagoranci taron karbarta zuwa jam’iyyar.
Shugaban Kungiyar Gwamnonin jam’iyyar APC kuma Gwamnan Jihar Kebbi, Atiku Bagudu da takwaransa na Jihar Imo, Hope Uzodinma da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ovie Omo-Agege na cikin wadanda suka halarci liyafar karbarta.
Akwai kuma dan takarar jam’iyyar a zaben Gwamnan Anambra, Sanata Andy Uba da shi ma ya halarci taron.
Daraktan Watsa Labarai na jam’iyyar, Malam Salisu Na’inna Dambatta wanda ya fitar da sanarwan bayan taron ga ’yan jarida, ya ce Mai Buni ya taya ta murnar tare da bata tabbacin cewa jam’iyyar za ta bata dukkan hakokki da ta cancanta kamar sauran mambobinta.
A jawabin da ta yi, sanata Oduah ta ce jamiyayar APC ta kawo sabon salo na sauyin siyasa a yankin Kudu Maso Gabas, da ba za ta bari a barta a baya ba.
Ta ce ta shigo jamiyyar ne tare da dumbin magoya bayanta.
Gwamnan Jihar Imo, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Yakin Neman Zaben Gwamnan Anambra na jam’iyyar APC da za a gudanar a watan Nuwamba, ya ce ya na da yakinin cewa jam’iyyarsu za ta samu nasara a yayin zaben.