Kasar Spain ta lallasa Ingila a wasan karshe na cin kofin kwallon kafa na duniya na mata inda ta lashe kofin a karon farko a tarihi.
Kwallon da ’yar wasa Olga Carmona ta ci a minti na 29 ce dai ta bai wa Spain nasarar a wasan da aka fafata ranar Lahadi.
- Fitattun ’yan kwallon da suka koma Saudiyya da taka leda
- Sai nan da shekara 3 za mu sauka daga mulki – Gwamnatin sojin Nijar
An dai buga wasan ne a Sydney, babban birnin kasar Austaraliya.
Tawagar ta kasar Spain dai ta rike wuta ne tun daga farkon wasan, inda duk yunkurin da matan na Ingila suka yi na farke kwallon ya ci tura har aka tashi wasan.
’Yar wasan nan ta Spain da ta taba lashe kambun Ballon d’Or ta duniya, Alexia Putellas dai an ajiye ta daga jerin ’yan wasan da suka buga wa kasarta wasan na karshe da Ingila.