Rundunar sojojin kasa ta Faransa ta sanar da kashe Soumana Boura, jagoran kungiyar IS a Jamhuriyyar Nijar.
Ma’aikatar Tsaron Faransa a ranar Talata ta sanar cewa Soumana Boura shi ne babban wanda ake zargi da kisan ma’aikatan agajin Faransa a kasar da ke yammacin Afirka a watan Agustan 2020.
- Aisha Buhari ta bai wa ma’aikatanta hutu har sai ta neme su
- Coronavirus: Tottenham ta fice daga gasar Europa Conference
Rundunar sojin kasa ta Faransa ta ce an samu nasarar kashe Boura ne a ranar Litinin, 20 ga watan Disamba yayin wani luguden wuta da dakarunta na rundunar Operation Barkhane mai kakkabe ayyukan yan ta’adda a Arewacin Tillaberi, wani yanki da ke Arewa maso Gabashin Nijar.
Bayanai sun ce kungiyar IS a Nijar karkashin jagorancin Boura ce ta dauki alhakin kisan wasu ma’aikatan agaji shida ’yan tsakanin shekara 25 zuwa 31 a watan Agustan bara.
An dai kashe ma’aikatan kungiyoyin agaji na fararen hula tare da wasu mutum biyu yayin da suka ziyarci gandun daji na Koure, mai nisan kilomita 65 daga Niamey, babban birnin Nijar.
Kanal Pascal Ianni, mai magana da yawun babban hafsan sojin kasa na Nijar ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa, Boura ya bayar da umarnin nadar bidiyon kisan mutanen takwas.
Bidiyon ya nuna yadda maharan suka yi wa wata mace daya daga cikin mutanen yankan rago, yayin da suka harbe ragowar sannan suka cinna wa motarsu wuta suka tsere.
Tun a wancan lokaci Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana cewa irin wannan kashe-kashe a fili hari ne na ta’addanci wanda kuma yana barazanar ramuwar gayya.
Mutuwar Boura tana zuwa ne watanni hudu bayan da sojojin Faransa suka sanar da mutuwar Adnan Abou Walid al-Sahrawi, shugaban kungiyar IS na yankin Sahara kuma wanda ake zargi da kitsa kazamin harin da aka kai wa ma’aikatan Faransa.
A watannin bayan nan ne aka kama wasu mutum 11 a Jamhuriyyar Nijar bisa zargi hannunsu a kisan gillar.