✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Murna ta ɓarke a Maigatari bayan Nijar ta buɗe iyakarta da Najeriya

Saura ƙiris na sauya matsugunni amma yanzu da aka buɗe kan iyakar na samu nutsuwa da kwanciyar hankali.

Murna ta ɓarke a garin Maigatari da ke makwabtaka da Jihar Jigawa bayan da Jamhuriyyar Nijar ta buɗe iyakarta da Najeriya.

Ja’afar Ismail Maigatari, wani ɗan kasuwa ya ce, kafin yanzu ya debe tsammani kan alaƙa tsakanin Nijar da Najeriya amma da ya ji labarin sake buɗe kan iyaka sai ya samu natsuwa da farin ciki.

A cewar Ismail, “Na so in bar yankin da ke kan iyaka zuwa wani wurin domin ci gaba da harkokina na kasuwanci, amma yanzu na samu nutsuwa da kwanciyar hankali.

“Ni da iyalina mun yi farin ciki tare da yin addu’a ga waɗanda suka taimaka wajen buɗe iyakar domin hakan zai ceci rayukan mutane da dama,” in ji Ja’afar.

Bashir Ibrahim, wani mai kasuwancin canjin kuɗi a garin Maigatari ya ce a yanzu ya manta da wahalar da ya sha bayan rufe iyakar.

“Ina kyautata zaton a wannan makon komai zai canza nan take, musamman a lokacin cin kasuwar Maigatari wadda aka saba yi a duk ranar Alhamis ta mako,” in ji Bashir.

Rayuwar al’ummar iyakar Maigatari ta koma yadda aka saba yayin da mazauna yankin ke murnar sake buɗe iyakar.

Ana iya tuna cewa, an dai rufe iyakar kasar da ke tsakanin makwabtan biyu biyo bayan juyin mulkin da aka yi a ranar 26 ga watan Yuli da kuma takunkumin da kungiyar ECOWAS ta kakaba mata, inda a yanzu Jamhuriyyar Nijar ta sake buɗe kan iyakarta da Najeriya a yankunan Diffa da Tahoua da Maradi da Dosso.

A wani sakon rediyo da aka watsa a shafukan sada zumunta, a ranar Alhamis, ma’aikatar harkokin cikin gida ta Jamhuriyar Nijar ta umurci gwamnonin waɗannan yankuna na kan iyaka da su ba da izinin sake bude aiki da karfe 12:00 na dare.

Ma’aikatar ta kuma umurci gwamnonin da abin ya shafa da su karfafa tsaro a kan iyakokin kasar.

An buɗe iyakokin Najeriya makonnin da suka gabata bayan ɗage takunkumin da kungiyar ECOWAS ta kakabawa ƙasar a wani taro da aka yi a Abuja, amma Nijar ba ta mayar da martani ba nan take.