✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yau take Sallah a Nijar

Da maraicen ranar Litinin hukumomi suka sanar da ganin jinjirin watan Shawwal a Nijar.

A wannan Talatar ake gudanar da bikin ƙaramar sallah a Jamhuriyar Nijar bayan hukumomi sun bayyana ganin jaririn watan Shawwal.

Da maraicen ranar Litinin ce Majalisar Ƙoli ta Addinin Musulunci ta Jamhuriyar Nijar ta ce an ga watan Shawwal a jihohi biyar na ƙasar.

Wannan sanarwar ta fito ne daga babban sakataren dindindin na Majalisar Musulunci ta Nijar, Abdramane Tidjani, a gidan talabijin na kasar.

A cewar Majalisar Musulunci, an ga jinjirin wata a wasu yankuna da dama na ƙasar, irinsu Rural Commune of Bangui a Madaoua, gundumar Misrata ta Agadez, da gundumar Tchirozérine, da Diffa da Tesker kabirou Yarima.

Dalilin haka ne ta bayar da umarni a gudanar da sallar idin ƙaramar sallah a ranar Talata, 1 ga watan Shawwal, 1445 daidai da 9 ga watan Afrilun 2024.

Majalisar Ƙoli ta Addinin Musulunci ta yi roƙon Allah Ya karɓi ibadun da aka yi a watan Ramadan, sannan ta yi kira ga ’yan Nijar su ci gaba da yi wa ƙasar addu’o’in fatan alheri.

Wannan na zuwa ne a yayin da aka sanar da rashin ganin watan Shawwal a galibin ƙasashen duniya, abin da ya sa hukumomi suka ayyana ranar Laraba, 10 ga watan Afrilu a matsayin ranar ƙaramar Sallah.

Ƙasashen da za su yi karamar sallah ranar Laraba sun haɗa da Nijeriya da Saudiyya da Falasɗinu da Qatar, da Iraƙi da Kuwait, da Masar, da Syria, da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.