Hukumar Kula da Ingancin Kaya ta Kasa (SON) ta gargadi masana’antu da su guji yin kaya marasa inganci don tabbatar da lafiyar al’umma da dukiya ko ta rufe su.
Darakta-Janar na Hukumar, Ifeanyin Chukwunonso Okeke ne ya yi wannan gargadi yayin da hukumar ta raba wa kamfanoni 57 shaidar tabbatar da ingancin kayansu tare da karrama su a Kano.
Babban daraktan wanda ya samu wakilcin shugaban shiyya na Kano, Albert Wilberforce ya ce, “ba burinmu ba ne mu rufe masana’antu musamman masu tasowa.
“Aikinmu shi ne saka su a kan hanya ta yadda za su yi abin da ya dace kuma su samu lasisi da shaidar inganci.
“Burinmu shi ne mu ga al’umma sun aminta da kayanmu na gida, kasuwanci yana ci gab, wanda hakan zai taimaka wajen habbaka bunkasa kasuwanci da tattalin arziki a kasa.
“To amma, idan su masu wadannan masana’antu suka yi kunnen kashi, ba mu da wani zabi face mu rufe masana’antun nasu kuma mu hukunta su domin ya zama izina ga sauran, saboda ba za mu bari al’umma ta cutu ko ta yi asara ba.”
Ya kara da cewar wannan mataki shi ne na karshe domin ba burin hukumar ba ne a durkusar da harkokin kasuwanci.
Da yake nashi jawabin, shugaban masana’antu masu zaman kansu da ke Bompai da Jigawa, Muhammad Bello Isyaku ya ja hankalin masu sarrafa kaya da su tabbatar suna samar da kaya masu inganci don cin gajiyar tallafi da damarmaki da dama.
Ya kara da cewa, duk kamfanin da ba shi da shaidar inganci da lasisi yana wahala ya samu tagomashi, fitar da kaya kasahen waje ko cin gajiyar tallafi.