Masana’antun Nijeriya sun yi kwantan kayan Naira tiriliyan 1.24 a wata shida na farkon shekarar nan ta 2024 da muke ciki.
Kungiyar Masana’antu ta Nijeriya (MAN) ta bayyana cewa yawan kayan da suka yi kwantai ya ninka na shekarar da ta gabata sau uku da rabi, idan kayan biliyan 271 suka yi kwantai.
Rahoton Kungiyar MAN na yanayin tattalin arzikin wata shida na farkon 2023 da ta fitar ranar Litinin ya dora alhakin asarar a kan rashin karfin aljihun jama’a a sakamakon matsin tattalin arzikin da ake fama da shi a kasar, tun bayan janye tallafin mai da sauran matakan tattalin tattalin arziki da gwamnati ta dauka.
Sai dai ta ce duk da haka, yawan kayan da masana’antu ke samarwa a Nijeriya a shekara ya karu zuwa Naira tiriliyan 5.34, kashi 30.48% a 2024.
- Mun biya bashin N63bn da Ganduje ya karɓo — Gwamnatin Kano
- Masu hakar ma’adinai 13 sun rasu bayan ruftawar kasa a Filato
- Lakurawa na da jirgi mara matuki, sun karɓe iko a kauyukan Kebbi —Bukarti
Rahoton ya nuna cewa, “karuwar ta samu ne a sakamon tashin farashin kaya a cikin gida, inda aka samu karin kashi 34.19 a watan Yunin 2024.”
Ya kuma alakanta kwantai da kayan suka yi da da hauhawar farashin kaya da raguwar karfin aljihun masu sayen kaya da cire tallafin mai da kuma faduwar darajar Naira.
“Yawan kayan da suka yi kwantai ya nuna irin matsin da jama’a suke ciki, wanda ke bukatar a ba su tallafi domin su samu damar sayen kayan da suke bukata, wanda hakan zai habaka bangaren masana’antu,” in ji rahoton.
Ya bayyana cewa ninka kudin wutar lantarki da aka yi ya taka muhimmiyar rawa wajen hauhawar farashin kayan da masana’antu ke samarwa.
“Kazalika, kudin sayen man janareto da sauran hanyoyin samar da lantarki da makamashi a masana’antu sai karuwa yake ta yi, inda masu masana’antu suka kashe Naira biliyan 238.31 a wata shidan farkon 2024, wanda ya zarce na watanni shidan karshen 2023 da kashi 7.69%.
“Abin da ya kawo hakan shi ne karin kudin mai da sauran makamashi da masana’antu suke bukata saboda rashin tabbacin samun wutar lantarki na gwamnati,” a cewar rahoton.
Ya kuma koka bisa yadda karfin masana’antu na daukar ma’aikata ke ta raguwa, inda a watanni shidan farkon 2024, ayyuka 2,606 kacal suka samar, wanda ya gaza na kwatankwacin lokacin na 2023 da 29.99%.
“Samar da ayyuka a shekara ya ragu da 37.83%, wanda ke nuna tasirin kalubalen da masana’antu ke fusktanta, na rashin tabbas a tattalni arziki da tsadar kaya da kuma rashin yanayin kasuwanci mai sauki.
“Bangaren hada sanidarai da magunguna ne ya fi samar da ayyuka, a daya hannun kuma a masana’antun kerawa da hada motoci ne suka fi karanci wajen samar da ayyuka,” in ji rahoton.
Ya ci gaba da cewa a watanni shidan farkon 2024 masana’antu su fuskanci kalubalen tsadar kudin gudanarewa da kuma rashin ciniki da hauhawar farashin.
Duk da cewa wasu masana’antun sun jure, wannan yanayi, karfin wasu da dama ya ragu, da baya ga kwantan kaya da sallamar ma’aikata.
Rahoton ya ce “Wannan ya nuna muhimmancin Nijeriya ta dauki kwararan matakan magance wadannan matsalolin tattalin arziki, ta hanyar dokoki da tsare-tsare, inganta yanayin kasuwanci da fadada hanyoyin bunkasa tattalin arziki.
“Nasarar wadannan za ta shawon kan wannan yanayi tare da samar da ayyukan yi da rage tsadar kaya da inganta yanayin rayuwar ’yan Nijeriya.”