✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

SON ta gargadi masana’antu kan bi ka’idoji wajen sarrafa kayayyaki

Hukumar ta bayyana haka ne lokacin bikin bayar da takardar shaida ga kamfanoni 52 cika ƙa'idojin a Kano.

Hukumar Daidaita Ma’auni ta Najeriya (SON), ta yi kira ga masana’antu da su tabbatar da cewa kayayyakin da suke samarwa suna bin ƙa’idojin da aka tsara a Daidaitattun Ma’aunin Masana’antu na Najeriya (NIS).

Babban Daraktan SON, Dakta Ifeanyi Chukwunonso Okeke ne, ya yi wannan kira a lokacin bikin bayar da takardar shaida ga kamfanoni 52 da suka cika ka’idojin Shirin Tantance Kayayyaki (MANCAP) a Kano.

Wakilin Babban Daraktan, Ko’odinetan SON na Kano II, Dakta Ado Ibrahim, ya bayyana cewar takardar shaidar babba alama ce ga masana’antu.

“Takardar shaidar MANCAP ba kawai alamar yabo ba ce, tabbaci ne ga masu amfani da kayayyaki cewa an yi gwajin kayayyakinku kuma sun cika ka’idoji.

“Wannan yana nuna cewa kamfaninku na iya samar da kayayyaki masu inganci da za su gamsar da bukatun kwastomomi.

“Yau da muke taro a nan, muna jinjina wa kamfanoninku saboda wannan nasara. Amma ya zama wajibi ku ci gaba da samar da kayayyakin da suka dace da ka’idojin NIS.

“Wannan nasarar tana nuni da cewa kamfaninku yana da sha’awar samar da inganci, tsaro, da kuma gamsuwar kwastomomi.”

Ibrahim ya ƙara da cewa: “Shigarku cikin wannan shiri na MANCAP ba kawai ya inganta darajar kamfaninku ba, har da taimakawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasa.

“Don haka, ina kira a gare ku da ku dage wajen samar da inganci a kowane lokaci. Hukumar SON a shirye take ta tallafa muku ta hanyar shirye-shirye da tsare-tsarenmu daban-daban.”

Shi ma Ko’odinetan SON na Kano na I, Roger John, ya gargadi kamfanonin da aka bai wa takardar shaidar da su kiyaye ka’idojin da aka shimfida musu.

“Ina kiran ku da ku tabbatar da cewa kuna bin duk ka’idojin da suka sa ku samu wannan takardar shaida.

“Dole ku ci gaba da inganta hanyoyin da kuka bi wajen samar da kayayyakin ku.

“Wannan takardar shaida tana nuna cewa kayayyakin ku sun dace kuma za su amfanar ’yan Najeriya. Amma ku sani cewa ba ta dauwama.

“Idan har aka gano cewa kayayyakin da kuke samarwa ba su kai matsayin da ake bukata ba, za a iya karbe wannan takardar. Saboda haka, dole ku dage wajen samar da kayayyaki masu ingancia kowane lokaci.”