✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Son Manzon Allah (SAW) ibada ne

Babban Masallacin NASFAT, Abuja Fassarar Salihu Makera Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Mai rahama Mai jinkai. Mai nuna mulki Ranar Sakamako. Kai kadai…

Babban Masallacin NASFAT, Abuja

Fassarar Salihu Makera

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Mai rahama Mai jinkai. Mai nuna mulki Ranar Sakamako. Kai kadai muke bautawa kuma gare Ka kadai muke neman taimako. Ka shiryar da mu hanya madaidaiciya. Hanyar wadanda Ka yi wa ni’ima, ba wadanda Ka yi fushi a kansu ba, kuma ba batattu ba. Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai Yake ba Ya da abokin tarayya a gare Shi, Wanda Yake cewa: “Annabi ne mafi cancanta ga muminai bisa ga su kansu, kuma matansa uwayensu ne.” Kuma na shaida lallai Shugabanmu, masoyinmu, abin koyinmu, zababbenmu kuma jagoranmu Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa, wanda aka aiko shi a matsayin rahama ga dukan halittu. Ya Ubangiji! Ka yi tsira da aminci a kan shugabanmu Annabi Muhammad da alayen Muhammad. Ya Ubangiji! Ka yi albarka a kan Muhammad da alayen Muhammad, Ya Ubangiji! Ka yi rahama a kan Muhammad da alayen Muhammad, kamar yadda Ka yi tsira da rahama da albarka a kan shugabanmu Annabi Ibrahim da alayen Ibrahim a cikin talikai. Lallai ne Kai ne Abin godiya, Mai girma.

Bayan haka, ya ku bayin Allah! Ina yi muku wasiyya da ni kaina da yi wa Allah takawa da kuma son Annabinku Muhammad (SAW).

Son Annabi wajibi ne a kan kowane Musulmi, mumini, muhsini mai kadaita Allah mai bin Annabi Muhammad (SAW). Da soyayyarsa ce ake samun kyautar Ubangiji. Kuma yana daga cikin ginshikan ka’idojin imani a so Manzon Allah (SAW), son da Annabin Allah (SAW) ya bayyana shi a cikin fadinsa mai girma: “Bawa bai zamowa mai imani har sai na kasance mafi soyuwa gare shi daga iyalinsa da dukiyarsa da mutane baki daya.”

“Annabi ne mafi cancanta ga muminai bisa ga su kansu.”

Wajibcin son Annabi (SAW):

Son Annabi (SAW) ba kamar sauran nau’o’in soyayya ba ne da ake yi ga kowane mutum, lallai son Annabi (SAW) ibada ce, mai girma da muke bauta wa Allah Madaukaki da ita, neman kusanci ne da muke kusantar Allah da shi, babba ne daga cikin usulun addini.

Mai tsira da Amincin Allah ya ce: “Wallahi dayanku ba zai zamo mai imani ba, har sai na fi soyuwa a gare shi daga kansa da dukiyarsa da ’ya’yansa da dukan mutane.” A cikin sahihi har wa yau, lallai Umar (RA) ya ce: “Ya Manzon Allah, wallahi kai ne mafi soyuwa a gare ni daga dukan komai baya ga raina. Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: A’a ya Umar, har sai na kasance na fi soyuwa a gare ka daga ranka.” Sai Umar ya ce: “Ya Manzon Allah! Wallahi kai ne mafi soyuwa a gare ni daga dukan komai hatta raina.” Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Yanzu (imaninka ya cika) ya Umar.”

Al’amarin sonsa (SAW) ba al’amari ne na zabi ba da in mutum ya ga dama zai so shi, in ya ga dama ya ki sonsa. A’a wajibi ne a kan kowane Musulmi kuma yana daga cikin ginshikan imani da babu makawa wannan soyayya ta kasance mafi karfi daga dukkan soyayya koda son mutum ga kashin kansa.

Allah Madaukaki Ya ce: “Ka ce idan kun kasance kuna son Allah, to ku bi ni sai Allah Ya so ku, kuma Ya gafarta muku zunubanku. Kuma Allah Mai gafara ne Mai jinkai.”

Kuma Madaukaki Ya ce: “Ku yi da’a ga Allah kuma ku yi da’a ga Manzon (nan), idan kuka juya baya, to lallai ne Allah ba Ya son kafirai.” Kuma Ya sake cewa: “Kuma Allah da ManzonSa ne mafi cancanta ku yardar da Shi, idan kun kasance masu imani.”

Ashe ba Allah ne Ya umarci muminai da yin salati da taslimi a gare shi (SAW) ba? Shi ne Wanda Yake salati a kansa, Shi da mala’ikunSa. “Lallai Allah da mala’ikunSa suna salati ga Annabi. Ya ku wadanda suka yi imani! Ku yi salati a gare shi, kuma ku yi sallama domin amintarwa a gare shi.”

Don haka Manzon Allah ne ya fi dacewa a so shi. Kada mu manta wata rana (SAW) ya shiga kasuwa sai ya ji wani yana kira wa zai saye shi, ubangidansa yana cewa wa zai sayi bawansa. Bawan yana cewa a saye shi daga wanda yake hana shi yin salati, sai wani ya saye shi, lokacin da ya hadu da jinya Annabi (SAW) da kansa ya je gaida shi, kuma da ya rasu Annabi (SAW) ya yi masa Sallar Janaza da kansa, saboda me saboda yi wa Annabi (SAW) salati, ibada ce.

Yaya ba za mu so ka ba ya Manzon Allah! Alhali ba za mu manta ranar da ka shiga ga Sauban, wani saurayi mai tawali’u fakiri, ka iske shi yana mai bakin ciki yana kuka, ka tambaye shi, me yake sa ka kuka ya Sauban? Ya ce Ya Manzon Allah! Lallai kai idan ba ka kusa da ni, sai inji shaukinka, sai idanuwana su rika zubar da hawaye. Sai kuma in rika tuna Lahira, hakika ina tunanin zan yi nesa da kai a cikin Aljanna saboda kai za ka kasance a cikin mafi daukakarta, sai kukana ya karu. Sai take a lokacin Jibrilu amintacce ya sauko cewa Allah Madaukai Yana cewa: “Wanda ya yi da’a ga Allah da Manzon (nan), to wadancan suna tare da wadanda Allah Ya yi ni’ima a kansu na daga annabawa da siddikai da shahidai da salihai, kuma wannan tarayya ta yi kyau. Wannan falala ce daga Allah, kuma Allah Ya isa ya zama Masani.”

Lahaula wala kuwwata illa billahil aliyil azim.

 

Huduba ta Biyu:

Dalilin da muke son Annabi (SAW)

  1. Saboda neman dacewa da muradin Allah Madaukaki wajen sonsa. Saboda Manzon Allah (SAW) shi ne mafi soyuwar halitta a wurin Allah Madaukaki. Hakika Allah Ya rike shi a matsayin masoyi kuma Ya yi yabo a kansa yabon da bai yi wa waninsa ba. Don haka ya zama wajibi a kan kowane Musulmi ya so abin da Allah Yake so, kuma hakan yana daga cikin cikar soyayya ga Allah Madaukaki.
  2. Cikar imani: Manzon Allah (SAW) ya riga ya bayyana cewa son Annabi (SAW) da girmama shi da fifita shi a kan kowa da komai cikar imani ne. “Na rantse da Wanda raina yake hannunSa dayanku ba zai zamo mai imani ba, har sai na fi soyuwa a gare shi daga kansa da dukiyarsa da ’ya’yansa da dukan mutane.”
  3. Bambancin Annabi (SAW) da sauran mutane: Manzon Allah (SAW) shi ne mafi daukakar mutane mafi karimcin mutane mafi tsarkin mutane mafi girman mutane a cikin komai. Wannan ya isa SAW ya kasance mafi soyuwa a wurin mutane.
  4. Tsananin sonsa ga al’ummarsa da tausaya mata da rahamarsa a gare ta: Kamar yadda Allah Ya siffanta shi a cikin fadinSa: “Hakika Manzo daga cikinku ya je muku. Abin da kuka wahala da shi mai nauyi ne a kansa. Mai kwadayi ne saboda ku. Ga muminai mai tausayi mai jin kai.” Domin haka ne ake fatar samun cetonsa a gobe Kiyama.
  5. Baza kokarinsa wajen kiran al’ummarsa, tare da fitar da mutane daga duffan zalunci zuwa hasken imani.

Son (SAW) shi ne komai.

  1. Gabatar da Annabi (SAW) a kan kowa:

Allah Madaukaki Ya ce: “Ya ku wadanda suka yi imani! Kada ku gabata (da komai) gaba Allah da ManzonSa, kuma ku yi da’a ga Allah da takawa. Lallai Allah Mai ji ne, Masani.” Kuma Ya ce: “Kuma idan ya kasance iyayenku da ’ya’yanku…..har zuwa karshen ayar” Don haka alamar son Annabi (SAW) ita ce kada a gabatar da wani abu ko yaya yake a gaba da Allah da ManzonSa (SAW).

  1. Yin ladabi gare shi (SAW):

Yin yabo a gare shi da yi masa salati saboda fadinSa Madaukaki: “Lallai Allah da mala’ikunsa….”  A rika ladabi yayin ambatonsa kada a ambace shi gatsau da sunansa kawai ba tare da an hada da annabta ko manzanci ba.

Yin ladabi a masallacinsa da raudarsa da barin yin maganganu ko daga murya a wuraren.

Girmama hadisansa da yin ladabi lokacin da ake saurarensu ko ake karanta su kamar yadda magabatan wannan al’umma suka yi. – Misali Malik, idan zai zauna don karanta Hadisi sai ya yi alwala irin ta Sallah ya sanya mafi kyan tufafinsa ya sanya turare ya taje gemunsa. Aka ce masa me ya sa kake haka? Sai ya ce ina girmama Hadisin Manzon Allah ne (SAW) da haka. Kuma Sa’id bn Musayyib ya kasance ba ya da lafiya yana cewa: “Ku daga ni, domin abin yana da girma a wurina in karanta wani Hadisin Manzon Allah (SAW) ina kwance.”

  1. Gaskata shi (SAW) cikin abin da ya bayar da labari:

Kamar yadda Abubakar (RA) ya yi lokacin Isra’i da Mi’iraji.

  1. Bin sa da yi masa da’a da bin shiriyarsa (SAW):

Yin da’a ga Manzon Allah (SAW) nuna misali ne na soyayya da gaskiyar soyayya a gare shi (SAW), kan haka ne Allah Madaukaki Ya ce: “Ka ce idan kun kasance kuna son Allah, to ku bi ni sai Allah Ya so ku, kuma Ya gafarta muku zunubanku. Kuma Allah Mai gafara ne Mai jinkai.” Muminin da yake son Annabi (SAW) shi ne wanda yake koyi da shi a cikin dukkan komai na ibada da halaye da dabi’u da mu’amala da ladubba.

  1. Kare shi (SAW):

Kare shi da dukiya da ’ya’ya da rai a cikin abin da ya shafi tsanani da abin ki “… kuma suna taimakon Allah da ManzonSa…”

  1. Taimaka wa da’awarsa da sakonsa da dukan abin da mutum ya mallaka na dukiya da rai.
  2. Kare Sunnarsa (SAW) ta wajen kiyaye ta da tsare ta.
  3. Yada Sunnarsa (SAW).

“Lallai Allah Yana umarni da adalci da kyautatawa da ba ma’abucin zumunta hakkinsa, kuma Yana hani daga alfasha da abin ki da zalunci. Yana yi muku wa’azi tsammaninku kuna tunawa.”

Allah Ya yi mana gafara ni da ku.

Za a iya samun Imam Sharafuddeen Aliagan ta tarho mai lamba 08034710862