Gwamna Douye Diri na Jihar Bayelsa ya ce zai daukaka kara domin nuna rashin gamsuwa da hukuncin da Kotun Sauraron Kararrakin Zaben ta yanke na soke zabensa a matsayin gwamnan Bayelsa.
Gwamna Diri ya bayyana hakan ne jim kadan bayan kotun ta sanar da soke zaben, inda ya ce Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ce ta yi kuskuren cire Jam’iyyar ANDP a zaben na 16 ga watan Nuwamban bara.
A cewar Mukaddashin Sakataren Watsa Labaransa, Daniel Alabrah, gwamnan yana da yakinin zai samu nasara a Kotun Daukaka Kara, sannan ya bukaci mutane da su kwantar da hankalinsu.
Aminiya ta ruwaito cewa Kotun Sauraron Kararrakin Zaben ta soke zaben gwamnan Bayelsa, inda ta bukaci a sake zabe nan da kwana 90.
Hukuncin dai ya biyo bayan koken da dan takarar Jam’iyyar ANDP, Mista Kinga George, ya shigar ne yana nuna rashin amincewa da gaza sanya sunansa a cikin ‘yan takara.