Rundunar sojojin Najeriya sun sake kama wasu mayakan Boko Haram 16 cikin su akwai manyan Kwamandoji biyu na Kungiyar lokacin da rundunar ta kaiwa mayakan wani samame a garin Pulka da ke Karamar Hukumar Gwoza a jihar Borno.
Jami’in watsa labarai na rundunar Kanal Aminu Iliyasu, ne ya sanar da hakan yau Talata a Abuja inda ya ce an kama Kwamandojin Boko Haram din ne a cikin garin Pulka.
Kanal Aminu, ya kara da cewa an samu nasarar kama mayakan Boko Haram din ne ta hadin gwiwar jami’an tsaron farin kaya da aka horar ‘Civilian Joint Task Force’ (CJTF) a jihar.