Dakarun Sojin Kasar Rasha sun fara ficewa daga Kazakhstan a ranar Alhamis bayan da Shugaba Vladimir Putin ya bayyana cewa aikinsu na kwantar da tarzomar da ta biyo bayan zanga-zangar kasar ya juye zuwa rikici ya kammala.
Putin, a cikin jawabinsa, ya ce aikin dakarun kungiyar tsaro ta CSTO ya kawo karshe a Kazakhstan bayan da aikinsu ya janyo ce-ce-kuce daga kasashen duniya ciki har da Amurka.
- Rufe Twitter: Yadda ’Yan Najeriya Suka Yi Asara, Gwamnati Ta Ci Riba
- Muddin ba a tashi tsaye ba, mayakan ISWAP za su fitini Najeriya —Zulum
Rundunar tsaron CSTO da ke matsayi iri daya da na NATO na kunshe da dakarun kasashe shida — Rasha, Belarus, Armenia da kuma Tajikistan baya ga Kyrgystan da Kazakhstan — wadanda suke aiki tare don dakile barazanar tsaro a tsakaninsu.
Sai dai aikinsu a wannan karon ya gamu da kakkausar suka musamman bayan tsoma bakin Amurka da ake ganin shi ya sake tunzura masu zanga-zangar ta Kazakhstan, dalilin da ya tilasta dakatar da aikin da ya zama irinsa na farko a tarihi.
A ganawar Shugaban Kungiyar CSTO kuma Ministan Rsaron Rasha, Sergei Shoigu da Shugaba Vladimir Putin, ya tabbatar da cewa dakarun za su fara ficewa daga Kazakhstan a ranar Laraba mai zuwam su kuma kammala a ranar 22 ga watan nan da muke ciki.
Tun da farko Shugaba Kassym-Jomart Tokayev ya bukaci shigar Rasha kasar don kwantar da rikicin, sai dai isar dakarun ya sauya salon rikicin.
’Yan kasar ta Kazakhstan sun fara zanga-zangar ce bayan gwamnatin kasar ta yi karin farashim man fetur, baya ga tsadar kayan masarufi da suka yi tashin gwauron zabo.