✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sojojin Nijar sun kashe ’yan Boko Haram da dama, sun kama wasu da ransu

Sojojin sun kuma kwato wasu mutanen da aka sace

Sojojin Jamhuriyar Nijar sun kai farmaki kan sansanin ‘yan ta’addan Boko Haram da ke Garin Wanzam, inda suka kashe da dama tare da kubutar da wasu da aka yi garkuwa da su.

Sojojin da ke yaki da ’yan ta’addan karkashin rundunar hadin gwiwa ta MNJTF a tafikin Chadi da ke fama da ayyukan ta’addancin ne suka kai farmakin.

Wani jami’in leken asiri ya shaida wa Zagazola Makama, wani mai sharhi kan harkokin tsaro kuma masani kan yaki da tayar da kayar baya a yankin Tafkin Chadi cewa sojojin sun yi aiki da sahihan bayanan sirri na cewa wasu ragowar ’yan tada kayar baya na sace mutane tare da neman kudin fansa a yankin gaba daya.

Majiyoyi sun ce harin na ba-zata ya kai ga kashe wasu daga cikin ’yan ta’adda tare da samun nasarar kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su wadanda daga baya aka sada su da iyalansu.

“Dakarun sun kai farmakin ne a lokacin da ’yan ta’addan suke dafa abinci yayin da wasunsu ke barci,” inji majiyar leken asirin.

Ya ce an kuma samu nasarar cafke biyu daga cikin ’yan ta’addan da ransu yana mai cewa, sojojin sun kuma samu nasarar kwato makamai, alburusai da makamin roka daga matsugunin ’yan ta’addan.