Rundunar Sojojin Ruwa ta Najeriya ta kammala shirye-shiryen kaddamar da jirgin ruwa na yaki da injiniyoyinta suka kera.
Wannan dai shi nekaro na uku da rundunar take kera jirgin yaki a cikin gida.
- Kamfani ya ba dan Shugaban DSS kyautar gidan N90m a Abuja
- An dawo da hanyoyin sadarwar da aka katse saboda matsalar tsaro a Kaduna
Injiniyoyin rundunar ne dai suka jagoranci aikin kera jirgin, bisa kulawar kamfanin Navy Dockyard Limited, mallakin rundunar da ke unguwar Victoria Island a Jihar Legas.
Ana dai sa ran jirgin zai taimaka wajen yakin da ake yi da ’yan fashin teku a gabar ruwan sassa daban-daban na kasar nan.
Kazalika, jirgin zai taimaka matuka wajen yaki da kowacce irin barazanar tsaro da kasar za ta iya fuskanta musamman a kan iyakokinta na ruwa.