Sojojin da ke mulki a kasar Mali sun yi alkawarin dawo da mulki ga farar hula nan da shekarar 2024, biyo bayan juyin mulkin da suka yi a kasar a watan Agustan 2020.
Soji dai sun kwace mulkin kasar a wani juyin mulki da suka yi a watan Agustan 2020, kuma suka gaza cika alkawarin gudanar da zabe a watan Fabrairu, wanda ya jawo musu takunkumi daga Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS).
- Musulmai na ci gaba da Allah-wadai da Indiya kan batanci ga Annabi
- Zaben 2023 zai raba gardama kan salon mulkin APC a Najeriya —Atiku
Sojojin dai sun ce takunkumin da ya soma aiki ranar Litinin, ya biyo bayan wani sabon babin yarjeniyoyi da kasar ta yi da kungiyar, kuma suna fata hakan ya sanya ECOWAS ta janye takunkumin da ta sanya wa kasar.
“Fara amfani da hukuncin shaida ce ta amincewar jagororin Malin su tattauna da Kungiyar”, inji kakakin da ya karanto hukuncin ECOWAS din.
Kungiyar ta ECOWAS ba ta yi gaggawar cewa komai kan hukuncin kwana 24 din ba a ranar Litinin din.
Wannan turka-turkar dai ta haifar da sabani tsakanin Mali da abokan huldarta, ciki har da Amurka da Faransa.
A hannu guda kuma gwamnatin sojojin da ke kasashen da ke makwabtaka da Malin, wato Burkina Faso da kuma Guinea, na fuskantar makamanciyar barazanar daga ECOWAS din, bisa jan kafar da suke a dawo da mulkin Dimokuradiyya a kasashensu.