✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sojojin Isra’ila sun kashe Bafalasdine bayan sun zarge shi da caka musu wuka

Dag bisani kuma sun kama dan uwansa da mahaifiyarsa.

Sojojin Isra’ila sun harbe wani matashin Bafalasdine har lahira a kofar masallacin Al-Aqsa da ke birnin Kudus bayan sun zarge shi da caka wa biyu daga cikinsu wuka.

Lamarin dai ya faru ne daya daga cikin kofofin masallacin mai ssuna Bab Hutta, da wajen misalin karfe 4:30 na Asubar ranar Lahadi, a agogon can.

Kamfanin dillancin labaran Falasdinu mai suna Wafa ya rawaito cewa sunan matashin shi ne Kareem Jamal al-Qawasmi.

Likitocin da suka isa wajen jim kadan da faruwar lamarin ne suka tabbatar da rasuwarsa .

’Yan sandan Isra’ila dai sun yi zargin cewa mamacin ya ji wa biyu daga cikinsu rauni ta hanyar daba musu wuka.

Wani bidiyo da yake yawo a kafafen sada zumunta na zamani ya nuna gawar Kareem kwance a kasa bayan an harbe shi, kafin daga bisani wani Bayahude ya bi ka kansa, watakila don ya karasa shi.

Sai dai ba a iya tabbatar da sahihancin bidiyon ba.

Daga bisani dai dakarun Isra’ila sun garkame dukkan kofofin masallacin na Al-Aqsa bayan faruwar lamarin, kafi su sake bude su daga bisani.

Marigayin dai mazaunin yankin At-Tur ne da ke gabashin birnin na Kudus.

Kamfanin dillancin labaran na Wafa ya ce dakarun na Isra’ila sun kuma mamaye yankin ’yan sa’o’i kadan bayan kisan, inda suka kama dan uwan mamacin tare da mahaifiyarsa.

Ko a ranar daya ga watan Maris din 2022, said a wani sojan Isra’ila ya harbe wasu Falasdinawa uku a wurare daban-daban a birnin.

Bugu da kari, a ranar da lamarin ya faru, sojojin na Isra’ila sun kuma fatattaki wasu Musulmai da suke bukukuwan Isra’i da Mi’iraji a kofar Damascus da ke birnin na Kudus.

Akalla dai Falasdinawa 30 ne, ciki har da mata da kanana yara aka jikkata da harsasan roba a lokacin, sannan aka kama wasu 20 kuma.