✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojojin Gabon sun yi juyin mulki

Hakan ya biyo bayan nasarar da ya samu a zaɓen shugaban ƙasa a karo na uku.

Sojoji a ƙasar Gabon da ke yankin Tsakiyar Afirka sun ce sun yi wa shugaban ƙasa Ali Bongo juyin mulki.

Hakan ya biyo bayan nasarar da ya samu a zaɓen shugaban ƙasa a karo na uku.

Sojojin da suka bayyana a gidan talabijin na Gabon 24 sun ce sun soke zaɓen kuma sun rufe iyakokinsu da ƙasashe masu maƙwabtaka.

Sanarwar ta ce wanna shi ne matsayin daukacin rundunar sojin kasar, kuma sun “yi haka ne domin kare zaman lafiya a kasar nan ta hanyar kawo karshen wannan gwamnati.”

Masu yuyin mulkin sun kuma sanar da rushe duk hukumomi da masu rike da mukaman gwamnati sai abin da hali ya yi.

Bayan sanarwar tasu an yi ta jin karar harbi a sassan Libreville, babban birnin kasar, wanda ya jefa mazauna cikin zullumi.

Kawo yanzu babu wani martani da gwamnatin Gabon ta yi game da sanarwar juyin mulkin.

Wannan dai shi ne juyin mulki na biyu cikin wata guda a Afirka — kuma na biyar a shekara uku — bayan wanda aka yi a Nijar a watan da ya gabata.

Zaben shugaban kasa da na majalisar dokokin kasar da aka gudanar ranar Asabar ya kasance mai cike da rudani, inda Shugaba Ali Bongo ke neman tsawaita wa’adin mulkinsa a kasar, wadda danginsa suka shekara 56 suna mulki.

Rashin masu sanya ido daga kasashen waje da kuma matakin gwamnatin kasar na dakatar da wasu kafofin yada labarai na kasashen waje da kuma katse intanet sun haifar da damuwa game da zaben.

Da farko jam’iyyar adawa ta sanar da nasara a zaben kafin daga bisani hukumar zabe ta sanar da Bongo a matsayin wanda ya lashe zaben.